in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalar kiba ta kan kara barazanar kamuwa da ciwon sankara iri-iri 13
2017-04-05 14:10:11 cri

Wata kungiyar nazari karkashin shugabancin hukumar nazarin cutar sankara ta duniya ta yi shelar cewa, akwai wata alaka tsakanin matsalar kiba da kuma yiwuwar kamuwa da cutar sankara iri-iri har 8, inda jimilar nau'ikan cutar sankara da ka iya kama mutane sakamakon matsalar kiba ya kai guda 13 a yanzu.

Sai dai, kungiyar ta ce rage nauyin jiki yadda ya kamata yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da wadannan nau'ika na cutar sankara.

A shekarar 2002, Hukumar nazarin cutar sankara ta duniya dake karkashin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta yi nuni da cewa, akwai isassun alamomi da ke tabbatar da cewa, nauyin jiki da ya wuce misali yana da nasaba da cutar sankara dake kama uwar hanji, hangular makogwaro, koda, mama da mahaifa.

Masu nazari daga hukumar nazarin cutar sankara ta duniya sun tantance nazarce-nazarce fiye da guda dubu 1, wadanda aka gudanar domin gano alakar da ke tsakanin nauyin jiki da ya wuce misali da kuma barazanar kamuwa da ciwon sankara.

Sakamakon da suka samu ya nuna cewa, idan wani ko wata na sahun masu kiba ko kuma masu nauyin jikin da ya wuce misali, akwai yuwar kara fuskantar barazanar kamuwa da cutar sankara a tumbi, hanta, mama, saifa, kwan mace, kwakwalwa, Thyroid da bargo.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, yiwuwar kamuwa da cutar sankara wadda matsalar kiba ko nauyin jiki da ya wuce misali ke kawowa ya fi yadda ake zato a baya, tunda a baya, ba a san iri-iren cutar sankara da ke kama mutane sakamakon matsalar kiba ko nauyin jiki ya wuce misali ba.

Barazanar kamuwa da cutar sankara sakamakon matsalar kiba ko nauyin jiki ya wuce misali a tsakanin maza da mata, kuma wadanda su ka fito daga nahiyoyin arewacin Amurka, Turai, Asiya, yankin Gabas ta Tsakiya da ma sauran wasu wurare na daga cikin wadanda suka fi fuskantar irin wannan barazana.

Ina dalilin da ya sa matsalar kiba ko nauyin jiki da ya wuce misali zai kara barazanar kamuwa da ciwon sankara? Masu nazarin suna ganin cewa, akwai dalilai da yawa. Alal misali, yawan kibar da ake samu a jikin dan Adam ya kan sanya dan Adam ya fitar da sinadaran Female Hormone, Testosterone da Insulin fiye da kima, hakan ya kan kara haifar da hangula a jikin dan Adam, ta yadda cutar sankara ta kan kama dan Adam.

Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, watakila rayuwa ta hanyar da ta dace zai rage barazanar kamuwa da cuatar sankara sosai. To, mene ne ma'anar rayuwa ta hanyar da ta dace? Alal misali, cin abinci mai gina jiki, tabbatar da daidaiton nauyin jiki, motsa jiki kullum, da rashin shan taba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China