in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki yadda ya kamata yana iya rage barazanar da zauna cikin dogon lokaci yake haifarwa ga lafiyar dan Adam
2017-04-16 11:44:21 cri

Ban da yin barci, baligai masu yawa su kan zauna na tsawon lokaci, kamar tuka mota, ko yin aiki a ofis, ko kuma kallon TV a gida. A baya, masu ilmin lafiyar dan Adam sun yi gargadi da cewa, zama na tsawon lokaci kan yi barazana ga lafiyar dan Adam.

Wata kungiyar nazari mai kunshe da masu nazari daga kasashen Norway, Birtaniya, Australia da Amurka, ta gabatar da wani rahotonta a mujallar The Lancet ta Birtaniya. A cewar kungiyar, sun tantance sakamakon nazarce-nazarce guda 16 da aka gudanar a baya, wadanda suka shafi mutane fiye da miliyan 1, inda suka gano cewa, matsakaiciyar motsa jiki na awa daya a ko wace rana, yana iya rage barazanar da zama na dogon lokaci yake haifarwa ga lafiyar dan Adam.

To, mene ne ma'anar matsakaiciyar motsa jiki? Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, yin yawo da kafa mai nisan kilomita 5.6 a awa 1 ko kuma hawan keke mai saurin kilomita 16 a awa 1.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, motsa jiki a matsakaita cikin minti 60 zuwa 75 a ko wace rana, yana iya rage barazanar mutuwa da wuri sakamakon zama na fiye da awoyi 8 a ko wace rana. Duk da haka, yawancin mutane ba su iya jure irin wannan motsa jiki ba.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, a cikin mutanen da aka gudanar da nazarce-nazarcen a kansu, barazanar mutuwa da wuri da wadanda ba su motsa jiki sosai ba suke fuskanta ta fi wadanda su kan motsa jiki sosai yawa har da kashi 28 zuwa 59 cikin dari, duk da tsawon lokaci da sukan dauka a zaune. Ma iya cewa, wadanda ba su motsa jiki isasshe sun fi fuskantar barazanar ga lafiyarsu.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, mutane da yawa su kan je aiki cikin mota a ko wace rana, sa'an nan su zauna a ofis su yi aiki, sukan dauki tsawon lokaci a zaune. Ga irin wadannan mutane, masu nazarin sun yi ta jaddada muhimmancin motsa jiki. Ko yin yawo bayan cin abincin rana, ko gudu da sanyin safiya, ko kuma zuwa aiki kan keke, ya fi kyau a motsa jiki cikin awa daya a ko wace rana. To, idan ba a samu isasshen lokaci na motsa jiki ba, sai a dan motsa jiki kadan a ko wace rana, domin yana iya rage barazana ga lafiyar dan Adam. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China