in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Wang Yi a nahiyar Afirka ta bude wani sabon babin dangantaka tare da kasar Sin
2017-01-13 14:44:41 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri, ina fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna lafiya a birnin Beijing.

Hakika, ziyara ta musamman wacce ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya gudanar a kasashen Afirka biyar da suka hadar da kasar

Madagascar da Tanzania da jamhuriyar Kongo da Zambia da kuma tarayyar Nijeriya ta dau hankalin kasashen Turai da kuma masharhanta duba da irin tasirin da ziyarar ke da shi ta fuskar tattalin arziki da kara habaka dangantakar zumunta tsakanin bangarorin biyu.

Domin yayin da gwiwar kasashen Turai ke ci gaba da yin sanyi sakamakon yadda tasirin kasar Sin a nahiyar ke maye gurbin na yammacin duniya sannu a hankali, su kuwa masharhanta na ganin karuwar dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka, tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama. Domin za a iya cewa, kasar Sin ta kawo wa kasashen Afirka dauki ne a daidai lokacin da suke bukatar hakan, duba da yadda kalubaloli suka dabaibaye nahiyar ta ko'ina.

Ba shakka, wannan ziyara ta al'ada da firaministan na Sin ya saba kaiwa a nahiyar Afirka a farkon kowacce shekara ta kawar da duk wani shakku dangane da muhimmancin da kasar Sin ta dora ga dangantakar dake tsakanin ta da nahiyar Afirka. Lamarin dake haska cewa, Sin ta na bayar da fifikon musamman ga nahiyar Afirka, musamman yadda kasashen na Afirka ke nuna goyon bayan su kan manufar kasar Sin daya tak a fadin duniya.

Ban da wannan, idan aka yi duba da yarjeniyoyin ciniki guda 245 da Sin ta kulla da kasashen Afirka a shekarar bara ta 2016 kawai, wanda darajar yarjeniyoyi ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 50 ya kara bayyana girman dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ta fannoni da dama. Wanda kuma hakan na dada haska irin kyakkwan tanadin da Sin ta yi ga nahiyar ta Afirka.

A ra'ayi na, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a nahiyar Afirka duba da yadda hajojin kasar Sin ke kara nutsawa a kasuwannin Afirka bisa la'akari da cewa, a halin yanzu babu wasu kamfanoni dake iya samar da ababen more rayuwa da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum kan farashi mai rangwame kamar kamfanonin kasar Sin. Duk da haka, kasar Sin ba ta fasa bayar da horo ga kwararru ba duk da nufin taimaka wa nahiyar kaiwa ga gaci.

Wani abin burgewa shi ne, kasar Sin na ci gaba da kulla yarjeniyoyi ba ma kawai da gwamnatocin tsakiya ba, har ma da na jihohi musamman a kasa ta Nijeriya. Domin a makon da ya gabata ne, gwamnan jiha ta Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya dawo nan Nijeriya daga wata ziyarar aiki ta kimanin makonni biyu a kasar China, inda ya kulla wata yarjejeniyar samar da jirgin kasa a nan Kano da wani fitaccen kamfanin kera jiragen kasa na birnin Tianjin. Wannan ya kara tabbatar da cewa, dangantaka tsakanin Sin da Afirka na ci gaba da habaka kuma ya alamanta cewa akwai kyakkwar makoma dangane da haka.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China