in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da firaministan kasar Sin mr. Wang Yi zai fara a nahiyarmu ta Afirka su 5 ta ja hankalina sosai
2017-01-06 09:17:42 cri

Slm. 

Ziyarar da firaministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi zai fara yi a kasashenmu na Afirka su 5 a ranar 7 ga watan Janairu, 2017 da suka hada da: Madagaska, Zambia, Tanzania, Congo da kuma taraiyar Nigeria. A nawa ra'ayin, wannan ziyara wani muhimmin mataki ne kasar Sin ta dauka da zummar karfafa dangantakar dake akwai tsakanin kasashen su 5 da sabuwar nahiyar Sin ta zamani. Abunda ya fi jan hankalina bisa wannan ziyara ta mr. Wang Yi da tawagarsa, shine da ya fara yaye labulan ziyararsa ta farko a cikin sabuwar shekara ta 2017 da kai ziyara wasu kasashenmu na Afirka su 5. Babu shakka, wannan mataki da kasar Sin suka bada muhimmanci akai, ya alamunta cewa kasar Sin tana kaunar Afirka da jama'ar Afirka kana kuma hakan ya kara kuzarin kasar Sin da Afirka ta fannin diplomasiyya da kasuwanci da kuma inganta hulda abokantaka zuwa wani saban matakin yin hulda juna dan samun ci gaba mai daurewa. Muna fata cri Hausa za ku sa kaimi wajen gabatar mana da rahotanni da labaru masu dumi-dumi yayin ziyarar Firaministan kasar Sin mr. Wang Yi a wasu kasashenmu na Afirka.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China