in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barka da shekaru 75!
2016-12-03 12:01:43 cri
Assalamu alaikum CRI Hausa,

Gaisuwa mai tarin yawa da fatan alheri.

Yau shekaru 75 kenan da kafuwar CRI, mu kuma muna taya ku murna bisa namijin kokari da kwazo da kuka yi a cikin wadannan shekaru. Hakika, kun bayar da gudunmuwa sosai wajen ci gaba da kuma bunkasar CRI.

Ba ga CRI kawai kuka bada gudunmuwa ba, har ma ita kan ta kasar Sin ta amfana ainun da aikin ku na fadakarwa da fahimtar da Duniya abinda kasar ta kunsa, da kuma yada manufarta a fadin Duniya.

A shekarun baya, lokacin cikar shekaru 60 da kafuwar CRI, na samu halartar bukukuwan, abin ya kayatar sosai.

Ina yi muku fatan alheri da kuma taya ku murna a Yau da kuke bukin abin. Allah Ya taimaka.

Daga,

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China