in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murnar bikin tsakiyar kaka
2016-09-21 14:51:29 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya. Bayan haka, na aiko da wannan sako ne domin na taya al'ummar Sinawa murnar bikin tsakiyar kaka (Zhongqiu) na bana wanda ya zo daidai da 15 ga watan Satumba.

Hakika, na yi la'akari da cawa wannan biki yana da muhimmanci sosai ga al'ummar Sinawa, kasancewa shi ne biki na biyu mafi muhimmanci cikin dukkanin bukukuwan Sinawa. Saboda haka ina yi musu fatan alheri dangane da wannan biki mai muhimmanci. Ina kuma fatan dukkanin iyalai sun hadu da juna cikin farin ciki da walwala.

Ban da wannan, ina farin cikin shaida muku cewa na sauraroli shirin ku na 'Allah daya gari bamban' na ranar 16 ga wata wanda muka saurari bayani dangane da tarihin wannan biki na Zhongqiu da kuma yadda Sinawa suke gudanar da shi. Na ji dadin shirin sosai saboda ya kara min ilimi kuma ya kayatar da ni. Ina yi muku godiya ta musamman dangane da wannan kokari.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo

Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China