in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samun jinya ta hanyar shan magunguna kafin yin tiyata ya fi ba da taimako wajen yaki da ciwon kansa da ya kai matsayin karshe
2016-10-08 07:34:32 cri

Jami'ar London ta kasar Birtaniya ta kaddamar sakamakon nazari a kwanan baya, wanda sakamakon sa ya nuna cewa, yayin da ake ba da jinya ta hanyar shan magunguna ga wadanda suke fama da ciwon kansa lokacin da cutar ta kai matsayin karshe, kafin a yi musu tiyata, yana iya rage matsalolin da su kan biyo bayan tiyatar, kana kuma yana ba da taimako wajen kyautata zaman rayuwar masu fama da ciwon.

Masu nazari daga jami'ar London, da jami'ar Birmingham ta kasar, sun gudanar da wani gwaji na hadin gwiwa, inda mata dari biyar da hamsin suka shiga gwajin, cikin su 276 sun samu jinyar da aka saba yi yanzu bisa ma'auni, wato samun jinya ta hanyar shan magunguna har sau 6 bayan an yi musu tiyata. Sauran 274 kuma sun sha magungunan ne sau 3 kafin a yi musu tiyata.

Masu nazarin sun gano cewa, a cikin mata 276 da suka samu jinya ta hanyar shan magunguna har sau 6 bayan an yi musu tiyata, yawan wadanda suka gamu da matsalolin da suka biyo bayan tiyatar, da kuma yawan wadanda suka mutu cikin kwanaki 28 bayan da aka yi musu tiyatar, dukansu sun fi wadanda suka samu jinya ta hanyar shan magunguna sau 3 kafin a yi musu tiyatar. Haka zalika, sabuwar hanyar ba da jinya tana iya rage tsawon lokacin da majiyyatan suka yi sana jinya a asibiti, don haka majiyyatan za su koma zaman rayuwarsu cikin hanzari, sa'an nan za a iya yin tsimin kudi, da magani, da sauran kayayyakin kiwon lafiyar al'umma da ake amfani da su.

Masu nazarin na kasar Birtaniya sun yi bayani da cewa, gwajin da suka gudanar ya tabbatar da cewa, hana kumburar kari da ke cikin kwan mace, ta hanyar ba da jinya ta hanyar shan magunguna tukuna, daga baya a yi mata tiyata domin kau da karin daga jikinta, yana iya rage matsalolin da a kan gamu da su yayin da ake jinyar ta, da kuma tsawon lokacin samun jinya, wanda hakan zai zama wani ci gaba ga majiyyata baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China