in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin wasannin bidiyon nuna jarumta kullum yana iya taimakawa kwakwalwar dan Adam kara yin aiki yadda ya kamata
2016-08-21 13:05:28 cri

Masu nazari na kasar Sin sun kaddamar da rahotonsu a cikin "rahotannin kimiyya" na kasar Birtaniya a kwanan baya, inda a cewarsu, mutanen da kan yi wasannin bidiyon nuna jarumta kullum, mai yiwuwa wasu muhimman sassan da ke cikin kwakwalwarsu suna kara yin aiki sosai, lamarin da kila zai yi mana bayani kan dalilin da ya sa wadannan masu sha'awar wasannin bidiyon nuna jarumta suka fi yin fintikau ta fuskar cikakkiyar nitsuwa, da kuma yadda suke amfani da idanu da hannaye da kuma kafafu yadda ya kamata cikin daidaito.

Sakamakon nazarin da aka gudanar a baya ya yi nuni da cewa, wadanda su kan yin wasannin bidiyon nuna jarumta sun fi wadanda ba safai su kan yi wasannin ba nuna kwarewa a fannonin nuna cikakkiyar nitsuwa, da kuma yadda suke amfani da idanu da hannaye da kuma kafafu yadda ya kamata cikin daidaito, ko da yake ba a yi bayani kan alakar da ke tsakanin hakan da kuma sauyin kwakwalwar dan Adam ba.

Masu nazari daga jami'ar kimiyya da fasahar wutar lantarki ta kasar Sin, sun gayyaci wasu masu aikin sa kai rukunoni guda 2. A cikin rukuni na A, su 27, dukkansu masu sha'awar wasannin bidiyon nuna jarumta ne kwararru, wadanda suka kwashe shekaru fiye da 6 suna yin wasannin, haka kuma suna kan gaba a cikin lardunan da suke da zama, har ma da duk fadin kasar Sin a fannin yin wasannin bidiyon nuna jarumta. A cikin rukuni na B kuma, su 30 ba safai su kan yin wasannin ba, wato tsawon lokacin da suka dauka wajen fara yin wasannin bidiyon nuna jarumta bai kai shekara guda ba.

Masu nazarin sun kwatanta yanayin da wadannan masu aikin sa kai suke kasancewa a kwakwalwarsu, musamman ma wani bangare mai suna insula, wanda yake taka muhimmiyar rawa a fannonim cikakkiyar nitsuwar dan Adam, da kuma yadda muke amfani da idanu da hannaye da kuma kafafu yadda ya kamata cikin daidaito.

Masu nazarin sun gano cewa, in an kwatanta da wadanda ba safai su kan yi wasannin bidiyon nuna jarumta ba, wannan bangaren insula da ke cikin kwakwalwar wadansu daga kwararrun sun fin yin aiki yadda yadda ya kamata, sakamakon dogon lokaci da suka kwashe wajen yin wasannin bidiyon nuna jarumta.

Amma duk da haka, masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu, kwarya-kwaryar sakamako ne. Suna bukatar zurfafa nazarinsu, a kokarin kara sanin ainihin dalilin da ya sa hakan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China