in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daukar dogon lokaci wajen kallon shirye-shiryen telibijin, wani nau'in ciwo ne ga dan Adam
2016-08-08 07:56:08 cri

Masu karatu, ko kun taba daukar dogon lokaci wajen kallon shirye-shiryen telibijin? Amma wannan ba abun alfahari ba ne! Domin wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya shaida mana cewa, daukar dogon lokaci wajen kallon shirye-shiryen telibijin ya na da illa. A cewar sakamakon binciken wadanda suke yin hakan suna cikin yanayin kadaici da bakin ciki.

Masu nazari daga reshen Austin na jami'ar Texas ta Amurka sun kaddamar da rahotonsu game da wannan bincike ne a kwanan baya, inda a cewarsu, sun gudanar da nazari kan mutane 316, wadanda shekarunsu suka wuce 18 amma ba su kai 29 a duniya ba. Sun yi bincike kan yawan kallon shirye-shiryen telibijin da suka yi, da kuma yawan bakin ciki da suke ciki.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, idan bakin cikin mutum na karuwa, to, yana kara son kallon shirye-shiryen telibijin, a kokarin faranta ran sa. Wasu mutane kan kalli shirye-shiryen telibijin idan suna cikin bakin ciki, su kan kuma dauki awoyi ko kwanaki da dama a jere suna kallon shirye-shiryen telibijin da suke sha'awa ta na'urar telibijin, kamfuta ko na'urar DVD, a kokarin kubutar da kansu daga bakin ciki. Amma hakika dai abun da suke yi ba shi da amfani gare su wajen faranta rai, abun da ya kan kara sanya su bakin ciki. Haka kuma sakamakon daukar dogon lokaci wajen kallon shirye-shiryen telibijin na sa wadannan mutane su kara gazawa wajen gudanar da aiki cikin himma, da yin mu'amala da saura, har ma ba su da lokaci na yin hira da iyalansu.

A kasar Amurka, ana daukar mutanen da suke kallon shirye-shiryen telibijin fiye da guda 2 ba tare da tsayawa ba a ko wace rana, a matsayin masu son kallon TV. Amma a gaskiya mutane masu tarin yawa su kan kalli TV fiye da hakan. Wani dalibi da ke kasar Amurka ya taba yin shelar cewa, ya taba shafe makwanni guda 2 yana kallon shirye-shiryen telibijin guda 49, wato ke nan ya kalli shirye-shiryen telibijin guda 3 da rabi a ko wace rana.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, ana ganin cewa kallon wasu shirye-shiryen telibijin a gida, yana iya taimakawa mutane wajen samun sakin jiki, ko da kallon shirye-shiryen telibijin ya zama al'adarsu, to, ba damuwa, ba zai kawo illa ga lafiyarsu ba. Amma nazarin da muka ambato a baya ya nuna mana cewa, daukar dogon lokaci a gida wajen kallon shirye-shiryen telibijin fiye da kima, yana kawo illa ga lafiyar dan Adam a tunaninsu. Wasu kuma sun san illar yin hakan, amma ba su iya hana kansu yin hakan, lamarin da ya nuna cewa, masu son kallon shirye-shiryen telibijin ba su iya hana kansu. Har illa yau daukar dogon lokaci wajen kallon shirye-shiryen telibijin a zaune, yana sanya mutane su ji gajiya da samun kiba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China