in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 16 sun mutu da wuri sakamakon cututtuka marasa yaduwa a ko wace shekara
2016-09-12 15:25:11 cri

A cikin rahoton binciken da ta gudanar, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi bayani cewa, a ko wace shekara, ciwon zuciya, ciwon huhu, shan inna, cutar sankara, ciwon sukari da sauran cututtuka marasa yaduwa sun haddasa mutuwar mutane miliyan 16 kafin su cika shekaru 70 a duniya. Don haka hukumar WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace wajen sassauta manyan matsalolin da cututtuka marasa yaduwa suke haddasawa.

Rahoton ya yi nuni da cewa, ana iya ceton yawancin mutanen da suka mutu sakamakon irin wadannan cututtuka. A shekarar 2012, mutane miliyan 38 ne suka mutu sakamakon cututtuka marasa yaduwa, a cikinsu wasu miliyan 16 sun mutu tun kafin lokacin mutuwarsu, ma'ana ana iya ceton rayukansu tun da wuri.

Rahoton ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya su yi kira ga al'ummominsu da su rage shan taba da giya, tare da karfafa musu gwiwar cin abinci ta hanyar da ta dace, motsa jiki, fadada aiwatar da manufar kiwon lafiyar al'umma a duk fadin kasa, a kokarin rage mutuwar mutane sakamakon cututtuka marasa yaduwa.

A cewar Margret Chan, babbar darektan hukumar WHO, kasashen duniya suna da kyakkyawar dama ta kyautata yanayin da muke ciki a halin yanzu, wato kowa ne mutum ya ba da gudummawar dalar Amurka 1 zuwa 3 a ko wace shekara, hakan zai taimaka wajen rage barkewar cututtuka marasa yaduwa da kuma mutuwar mutane sosai.

Alkaluman da WHO ta fitar suna nuna cewa, kashi uku cikin kashi hudu na wadanda suka mutu sakamakon cututtuka marasa yaduwa sun fito ne daga kasashe masu karamin albashi da matsakaicin samu, inda kuma yawan wadanda suka mutu sakamakon cututtuka marasa yaduwa ya fi yawan wadanda suka mutu sakamakon cututtuka masu yaduwa. Saboda haka rahoton WHO ya yi kira ga gwamnatocin kasashe masu karamin albashi da matsakaicin samu da su kara daukar matakai na hana karuwar mutuwar mutane sakamakon cututtuka marasa yaduwa.

A yayin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 66 da ya gudana a shekarar 2013 ne, aka tsara wata manufar da ke cewa, ya zuwa shekarar 2025, za a rage yawan mutanen da suke mutuwa sakamakon cututtuka marasa yaduwa a fadin duniya da kashi 25 cikin dari. Ko da yake wasu kasashe suna kokarin cimma wannan manufa, amma kasashe da yankuna fiye da 60 ne kawai a duniya, wadanda suka karfafa gwiwar rage shan taba da giya,duk da cewa, akwai hanyoyi na kyautata wannan mataki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China