in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauro yana saurin cizon wasu mutane ne saboda yanayin kwayoyinsu na halitta
2016-09-05 10:38:07 cri

Wasu su kan yi kukan cewa, sauro yana saukin cizon su. To, wani sabon nazari da aka gudanar ya amsa irin wannan tambaya,kuma sakamakon bincken ya nuna cewa, watakila hakan ba zai rasa nasaba da yanayin kwayoyinsu na halitta ba.

Masu nazari daga kwalejin nazarin kiwon lafiya da ilmin likitanci na yankuna masu zafi da ke jami'ar London ta kasar Birtaniya sun gayyaci 'yan tagwaye wadanda suka yi kama da juna sosai 18 da kuma 'yan tagwayen da suka sha bamban da juna 19, inda suka ajiye sauro a cikin wani famfo mai siffar Y, daga baya suka sa karshen famfon guda 2 kan hannayen 'yan tagwayen, sai kuma suka duba hannun wanda sauro suka fi son ciza.

Sakamakon nazarinsu ya nuna mana cewa, a cikin 'yan tagwayen 18 din da suka yi kama da juna wadanda suke da kwayoyin halitta kusan iri daya, yiwuwar da suke fuskanta ta cizon sauro ta kusan yin daidai. Amma a cikin tagwayen da suka sha bamban da juna su 19 wadanda kwayoyinsu na halitta suka sha bamban da juna sosai, sun sha bamban sosai a fannin yadda sauron ke cizon su.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, tasirin da kwayoyin halitta suke haifarwa kan yadda ake saukin samun cizon sauro, ya kusan yin daidai da tasirin da kwayoyin halitta suke haifarwa kan tsayin jikin dan Adam.

Nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun nuna mana cewa, watakila wani nau'in kamshin dake fita daga jikin 'yan Adam da kuma abincin da mu ke ci, za su yi tasiri kan yadda sauro yake saukin cizon wasu. Sabon nazari da masu nazarin na kasar Birtaniya suka gudanar ya nuna mana cewa, watakila kwayoyin halitta sun fi taka muhimmiyar rawa, saboda suna sarrafa nau'in kamshin da ke fita daga jikinmu, lamarin da mai yiwuwa shi ne zai nuna ko saura zai fi saukin cizon mutum ko a'a.

A cikin wata sanarwa da masu nazarin suka fitar, sun yi bayani cewa, kara fahimtar dalilin da ya sa sauro ya ke saukin cizon wasu, yana taimakawa wajen fito da sabuwar hanyar kare dan Adam daga cizon sauro da kuma hana yaduwar cututtuka sakamakon cizon sauro, har ma a kai ga fito da sabon magani, ta hanyar amfani da wani nau'in kamshin da ke fitowa daga jikin dan Adam su fito da kamshin musamman na korar sauro daga jikinmu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China