in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsawon lokaci nawa ne da ya dace da yin barci a duhun dare?
2016-07-24 11:38:14 cri

Yin barci na da matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam, saboda muna daukar misalin sulusin lokacin rayukanmu wajen yin barci. Yau ma a cikin shirin, za mu tattauna muhimmancin barci ga koshin lafiyarmu!

Hakika yin barci mai tsawo ko maras tsawo dukansu ba suda kyau! Amma, abin tambaya shi ne, barcin sa'o'I nawa ya kamata mu yi a ko wace rana? Amsar ita ce gwargwadon ko wane mutum. Asusun kula da harkokin barci na kasar Amurka ya kaddamar da sabon littafin da ke yin jagora ga harkokin da suka shafi barci, inda ya gabatar da shawara daban daban.

Alal misali, babban nauyin jarirai sabbin haihuwa da kuma jariran da shekarunsu ba su wuce watanni 4 a duniya ba shi ne yin barci a ko wace rana. Suna bukatar sa'o'i 14 zuwa 17 suna yin barci a ko wace rana. Kananan yaran da shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 3 a duniya ba suna bukatar sa'o'i 11 zuwa 14 a ko wace rana suna yin barci. Yaran da shekarunsu suka wuce 6 amma ba su kai 14 a duniya ba suna bukatar sa'o'i 9 zuwa 11 a ko wace rana.

Matasa, suna cikin lokacin kuruciyarsu ne, wato suna kara bukatar yin barci! Don haka, ya kamata matasan da shekarunsu suka kai 14 amma ba su wuce 18 a duniya ba su yi barci na tsawon sa'o'i 8 zuwa 10 a ko wace rana. Duk da haka, idan sun yi barci na fiye da sa'o'i 11 a rana, to, hakan kan kawo illa ga lafiyarsu.

Ana bukatar baligai wadanda shekarunsu suka wuce 18 amma ba su kai 65 a duniya ba, su yi barci na tsawon sa'o'i 7 zuwa 9 a ko wace rana.

Ga wadanda shekarunsu suka wuce 65 da haihuwa kuwa, ana shawartarsu da su yi barci na tsawon sa'o'i 7 zuwa 8 a ko wace rana. Wasu tsoffafi su kan yi barci na sa'o'i 5 kawai, kullum sun tashi da wuri amma su kan ji barci da rana.

Hakika akwai bambanci a tsakanin ko wane mutum. Idan a kashegari ka ji garau, ba wani kasala, to, barcin da mutum ya yi ya isa ke nan!

To, yaya za a yi barci cikakken barci da dare? Ga wasu shawarwari da suka dace!

Da farko, kada a kwanta a makare, kana, kada a tashi daga barci a makare! Na biyu, kafin a yi barci, kada ka a yi amfani da na'urori masu amfani da wutar lantarki, kamar wayar salula, Ipad. Na uku, a dan sanyaya dakin da za a yi barci a ciki, kuma yana da kyau a yi wanka da ruwa mai dumi awa daya da rabi kafin a yi barci. Na hudu, yana da kyau a ci abincin dare da wuri. Na biyar, a rika motsa jiki lokaci-lokaci. Na shida, a yi bitar abubuwa masu faranta rai da suka faru a rana kafin a yi barci, a maimakon yawaita yin tunkiya. Na bakwai, a saurari kide-kide masu sanyaya zuciya, musamman ma kide-kiden gargajiya. Na takwas, a rika canja katifa bayan shekaru bakwai-bakwai. Na tara, a yi taka tsan-tsan wajen shan maganin barci. Na goma kuma, a karya kumallo yayin da ake jin dadin hasken rana da sanyin safiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China