in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila yin barci a makare yana sanya matasa su yi kiba
2016-07-21 17:25:17 cri

Masu nazari na kasar Amurka sun yi gargadi cewa, idan matasa su na barci a makare kullum, to, suna iya fuskantar barazanar yin kiba fiye da takwarorinsu wadanda kan yi barci da wuri.

A kwanan baya masu nazari daga reshen jami'ar Berkeley a California ta Amurka suka kaddamar da rahoton nazarin nasu, inda a cewarsu, sun tattara bayanan da suka shafi matasa da baligai fiye da dubu 3 da dari daga cikin bayanan da ke shafar lafiyar matasan Amurka, inda suka yi nazari kansu. An tattara wadannan bayanai ne cikin nazarin da aka fara gudanarwa tun daga shekarar 1994 kan dabi'ar matasan Amurka da lafiyar jikinsu da kuma tunani. An gudanar da nazarin ne a mabambantan lokuta guda 3, wato farkon lokacin kuruciyar matasan, lokacin da suke karatu a jami'a, da kuma farkon lokacin da suka balaga.

Masu nazarin sun kwatanta lokacin da matasan Amurka suka fara yin barci da dare da kuma mizanin nauyinsu wato BMI daga shekarar 1994 zuwa 2009, a kokarin gano alakar da ke tsakaninsu.

Mizanin BMI, ya kunshi awon nauyin mutum a ma'aunin kilogiram a raba da tsayin mutum bisa ma'aunin sikwaya mita. Mizanin BMI na mai koshin lafiya ya kan wuce maki 18.5 amma bai wuce maki 24.9 ba.

Masu nazarin sun gano cewa, tsawon barcin matasan Amurka da yawa, a kullum bai kai sa'o'i 9 ba. Idan matsakaicin tsawon lokacin barci ya ragu da sa'a daya a ko wane dare, to, mizanin BMI na matasan Amurka kan karu da maki 2.1 cikin shekaru 5. Haka kuma, motsa jiki, rage tsawon lokacin kallon telibijin da dai sauransu sun gaza wajen hana karuwar mizanin ma'aunin BMI.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, yayin da matasan suke girma sannu a hankali, wajibi ne su samu isasshen lokacin yin barci da dare, a kokarin tabbatar da daidaiton nauyin jikinsu. Matasan da suka saba yin barci da wuri da dare, bayan da suka cika mutum, galibi nauyinsu daidai ya ke. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China