in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watan azumin bana a kasar Sin
2016-06-06 14:27:55 cri

A shekaru 2 a jere, wato a shekarar bara da bara waccen, wasu kafufin yada labaru makiya kasar Sin, sun watsa wa duniya labarin karya inda suka ce, gwamnatin kasar Sin sun tilasta wa musulmai yan kabilar Ughuir cin abunci da rana tsaka a lokacin aiyukan ibadar watan azumi a jihar Xinjiang mai rinjayen musulmai a kasar Sin. Agaskiya wannan ba gaskiya ba ne, karya ce tsagoranta kana masu baza wannan labari marar tushe, sun yi hakan ne da zummar shafa wa gwamnatin kasar Sin bakin fenti a idanun al'ummar musulman duniya ta yadda karjini da kima da tagomashin kasar Sin da sinawa zai dusashe a duniyar musulmai. To, yana da kyau karatu a shafukan facebook da kafar jaridu da mujallu da su hattara da labarin jita-jita marar asali. A kasar Sin akwai manyan addinai guda 3 da suka hada da: addininmu na musulunci, kiristanci da kuma addinin Bhudda masu rinjaye a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Kana duk mabiya addinan 3, suna gudanar da aiyukan ibada a cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankali, ba tare da gwamnatin kasar Sin suna yi musu shishshi da katsa-landan a lamuransu addini ba. A duk fadin kasar Sin akwai musulmai kana akwai jihohi 3 da musulmai suke da rinjaye wayanda suka hada Da: Xinjiang, Xi'an da Ningxia. Haka nan, ina bada shawara ga cri Hausa da su bada himma sosai a lokacin aiyukan ibadar wata mai daraja na azumi wajen kara wayin kai ga mu al'ummar musulmai adangane da kokarin da makiya kasar Sin suke yi na dusashe tagomashin gwamnatin kasar Sin a duniyar musulmai.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa na jihar Yobe, taraiyar Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China