in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Togo ke yi a halin yanzu a kasar Sin, ya alamun kyakkyawar diplomasiyya da abokantaka dake akwai a shekaru 44 tsakanin kasashen 2 abokan juna
2016-06-01 09:04:35 cri

Ziyarar da shugaban kasar Togo a karshen mako a birnin Beijing na kasar Sin, ya kara alamunta kyakkyawar huldar amunci da abokantaka da kuma diplomasiyya dake akwai tsakanin kasashen 2 abokan juna. Kana wannan ziyara za ta kara karfafa huldar cinikaiya bisa manyan tsare-tsare da kuma kara kyautata hadin gwiwa bisa matakan samun bunkasuwa tare da juna a sabuwar dangantaka dake dada yaukaka a tsakanin kasashen Sin da Togo a halin yanzu. Kana wannan ziyara ta shugaban kasar Togo a kasar Sin ta kara bude wasu sabbin manyan shafuka a sabuwar dangantakar abokantaka dake akwai a tsakanin Sin da Togo. Kasar Sin da aminiyarta kasar Togo, sun kafa huldar diplomasiyya da cinikaiya da abokantaka da musayar al'adu kimanin shekaru 44 da suka gabata. A shekarar bara, kasar Sin ta kara jaddada matsayinta na yin hulda da Afirka kana Sin ta nuna kokari sosai wajen bada taimako ga kasashenmu na Afirka masu tasowa a lokacin da shugaban kasar Sin mista Xi Jinping ya gabatar da jawabai a taron kasashen Brics wanda ya guda a shekarar bara a kasar Afirka ta kudu. Hausawa suna cewa, yaban gwani ya zama dole, dan haka ina kara yaba wa mahukuntan kasar Sin bisa kokarinsu na samar da moriya ga kasashenmu na Afirka masu tasowa. Muna fata gwamnatin kasar Sin za su ci gaba da bada tallafi ga kasashenmu na Afirka masu tasowa, kamar yadda suke yi a halin yanzu.

Daga Malam Ali Buuge kiraji Gashua, daga jihar Yobe, taraiyar Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China