in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kasa da kasa kan yaki da cin hanci a birnin Tianjin na kasar Sin
2016-05-16 15:12:09 cri

Tarukan kasa da kasa da ya gudana a birnin Tianjin na kasar Sin a ranar alhamis 12 ga wata, adangane da yaki da cin hanci da karbar rashawa na kasashen duniya, ya alamunta matsayin koli da mahukuntan suka kai a dud duniya wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa. Tun farkon kafuwar sabuwar kasar Sin ta zamani a shekarar 1949, a zamanin mulkin marigayi shugaban kasar Sin Mao Zedong mahukuntan kasar Sin suka aiyana manyan matakai masu tsauri na yaki da cin hanci a kasar Sin inda suka kafa wata mujalla ta masamman da za ta dunga bibiyar laifukan cin hanci tare da lissafa sunayen manyan jami'an gwamnatin kasar Sin da aka kama da laifukan cin hanci da karbar rashawa domun yan kasa da ma duniya su gamsu da matakan da yaki da cin hanci da karbar rahawa a duk fadin kasar Sin. Yakamata sauran kasashen duniya takwarorin kasar Sin su hanzarta yin koyi da mahukuntan kasar Sin bisa matakan da suke dauka wajen girbe cin hanci da rashawa a kasar Sin.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China