in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddama kan tekun kudancin China ta dauki sabon salo
2016-05-13 10:18:14 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan CRI Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan Kano. Hakika, na ji dadin sauraron sabon shirin ku na GANI YA KORI JI na jiya Laraba 11 ga watan Mayu wanda malamai Maman Ada, Saminu Alassan da Ibrahim Yaya suka tattauna rikicin tekun kudancin China.

Ba shakka, malamai sun tattauna batutuwa masu muhimmanci dangane da wannan sa-toka sa-katsi kan mallakar yankin tekun kudancin China tun daga rikici tsakanin kasar Sin da kasashe makotan ta da kuma yadda kasashen ketare musamman kasar Amurka ke tsoma baki kan wannan takaddama.

A ra'ayi na, kasar Sin ta fi sauran kasashe da ke kudancin tekun China musamman kasar Philippines ikon mallakar iyakar teku bisa la'akari da hujjoji da suka hadar da tsohuwar taswirar kasa da Sinawa suka fitar a karni na 18 zamanin daular Qing ta gargajiya ya tabbatar da ikon mallakar mafi rinjayen kananan tsibirai da yankin tekun kudancin China.

Ban da wannan, bisa la'akari da girman kasa da kuma tsahon gabar teku na dubban kilomita fiye da sauran kasashen yankin ita ma shaida ce dake tabbatar da cewa, tun zamanin dauri kasar Sin tana da alaka da yankin kudancin tekun China.

A saboda haka, bai kamata kasashen da ke da iyaka da kasar Sin su rika tayar da jijiyar wuya ba ko kuma zama cikin fargabar fuskantar wani hari ko yaki daga China ba. Domin tarihi ya tabbatar da cewa, kasar Sin ba ta taba kai hari ko afkawa wata kasa da yaki ba, duk kuwa da cewa kasar Japan ta taba kai gari ga kasar Sin amma har kawo yanzu babu wani shirin kai ramuwar gayya da Sin ke yi kan Japan.

Lalle ya kamata kasar Sin ta sake tashi tsaye wajen kare kan iyakokinta ta kowanne hali, domin kasar Amurka na neman fakewa da guzuma domin ta harbi karsana. Wato ina nufin, Amurka na neman ta yi kutse cikin iyakokin tekun kasar Sin ta hanyar fakewa da wannan takaddama dake wanzuwa tsakanin kasashen Sin da Philippines. Domin ko a makon da mu ke ciki sai da dakarun da ke gadin iyakar teku na kasar Sin suka fatattaki wani jirgin ruwan yakin Amurka bayan da ya yi kutse a tekun kudancin China

Ina fatan za a kawo karshen wannan sa-in-sa tsakanin bangarorin biyu ta hanyar sulhu da shawarwarin kan tebur nan ba da dadewa ba.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China