in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari sabon shirin ku na GANI YA KORI JI
2016-04-25 08:47:52 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai dimbin yawa tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan CRI Hausa a birnin Beijing. Ba shakka, na samu zarafin sauraron sabon shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' na yau Laraba 6 ga watan Afrilu, wanda malamai Saminu Alhassan, Maman Ada da kuma Ahmad Inuwa Fagam suka tattauna yunkurin manyan kasashen duniya na hana 'yan tarzoma samun fusahar nukiliya, wato samar da cikakken tsaron nukiliya a doron kasa.

Gaskiya ni a ra'ayi na, wannan taro kan tsaron nukiliya da aka gudanar a kasar Amurka kamata ya yi ya ba da muhimmanci sosai wajen samar da manufofin da za su dakile fusahar ta nukiliya dungurungum, koda kuwa da nufin samar da makamashi ne, domin akwai babbar barazana da fusahar nukiliya ke yi ga makomar bil Adam da kuma muhalli. Kowa shaida ne na irin mummunar illar da gubar nukiliya ke yi ga muhalli a duk lokacin da aka samu aukuwar hatsari.

Bai kamata a mance da irin tsaka mai wuya da dan Adam ya samu kansa a ciki ba yayin da aka samu aukuwar hadarin nukiliya a kasar Rasha da kuma Japan. Inda aka samu bazuwar birbishin gubar nukiliya. Lamarin da ya kassara muhallin halittu matuka. Wannan yana daga cikin dalilan da a shekarar bara ta 2015 wasu masu rajin kare muhalli a kasar Jamus suka gudanar da zanga zangar nuna adawar su ga shirin firaministan Jamus wato Angela Makel na kafa sabuwar tashar nukiliya da nufin samar da makamashi a daya daga cikin biranen kasar.

Masu iya magana kan ce, Riga kafi ya fi magani, muddin ba a dakatar da bunkasa fusahar ta nukiliya ba koda wacce irin manufa kuwa, to la shakka, wata rana zai iya fadawa hannun masu tsatsauran ra'ayi. Hakan kuwa ba zai taba haifar da sakamako mai kyau ba ga duniya baki daya.

Don haka, ya dace masana kimiyya da fusaha su fara yin nazarin wata hanyar daban wajen samar da makamashi, domin tabbatar da cewa, an samu makamashi da ya dace da wannan zamani dake bayar da fifiko ga makamashi mai tsafta wanda ba ya gurbata muhalli. Bahaushe kan ce, "kowa ya kwana lafiya shi ya so".

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China