in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping a kasar Jamhuriyar Crech za ta bude wani sabbin shafukan tarishi a tsakanin kasashen 2 a cikin tsawon shekaru 67 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Crech
2016-04-25 08:47:35 cri

A ranar o6 ga watan October, 1949 ne, jamhuriyar jama'ar Sin da jamhuriyar Crech suka kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu bisa amuncewar juna dan kara dankon zumunci da abokantaka a tsakani bisa yakini. Kasashen 2 sun cimma manyan nasarori bisa matakan huldar jakadanci da yaukakar huldar diplomasiyyar da bunkasuwar tattalin arziki da musayar al'adu da ingiza matakan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a cikin shekaru 67 da kafuwar huldar deplomasiyya tsakanin kasar Sin da aminiyarsu kasar jamhuriyar Crech. Dan haka, wannan ziyara mai cike da tarishi da shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping da tawagarsa za su fara a ranar 28-30 ga watan March, 2o16 za ta kasance ziyara ta farko da wani shugaban kasar Sin ya taba kaiwa a kasar jamhuriyar Crech a tarishi tun bayan kafuwar huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2 a shekaru 67 da suka gabata. Muna fata ganawar da shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping zai yi da takwaransa na kasar jamhuriyar Crech mr. Milos Zeman, za ta kara bunkasuwar tattalin arzikin 2. A shekarar 2010, kasar sin da Jamhuriyar Crech sun kulla yarjejeniyar bunkasa tattalin arzikin kasashen 2 dan kara samun ci gaba ta fannin tattalin arziki mai karko a tsakanisu. Muna fata ziyarar shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping a kasar Jamhuriyar Crech za ta kafa fahimtar juna ta fannin siyasa, tattalin arziki da musar al'adu a tsakanin kasar Sin da aminiyarsu kasar jamhuriyar Crech.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China