in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki suna taimakawa wajen sassauta ciwon uwar hanji da jarirai ke fama da shi
2015-10-12 17:10:26 cri

Kwanan baya, jami'ar Turku ta kasar Finland ta gabatar da sakamakon wani nazari da ke nuna cewa wasu kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki, suna taimakawa wajen sassauta ciwon da jarirai ke fama da shi a uwar hanji.

Masu nazarin daga jami'ar sun zabi jarirai 30 da ka, wadanda shekarunsu ba su kai makonni 6 a duniya ba, kuma wadanda suka yi fama da ciwon uwar hanji. Sun shayar da wasu daga cikinsu wani nau'in karamar halitta mai rai kuma mai gina jiki wato LGG, yayin da suka shayar da sauran wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki, wanda likita kan baiwa mutumin da ke zaton ya kamu da wata cuta, ko lokacin da ake gwajin wani sabon magani. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, a bayyane take jariran da suka sha LGG sun dan dakatar da kukansu.

Har wa yau nazarin ya nuna mana cewa, kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki, suna ba da taimako wajen sassauta ciwon da jariran da aka haifa da wuri suke fama da shi a uwar hanji. An shigar da jarirai 94 da suka kasance cikin cikin mahaifansu mata har tsawon makonni 32 zuwa 36 cikin wannan nazari, inda masu nazarin suka gudanar da nazarin har na tsahon lokacin da jariran suka kai shekara guda a duniya. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, a cikin jariran da aka haifa a wuri, wadanda suka sha kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki, kashi 19 cikin dari ne kawai suka yi kuka sakamakon ciwon uwar hanji. Amma a cikin jariran da aka haifa wuri wadanda aka shayar da su wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki, wanda likita kan baiwa mutumin da ke zaton ya kamu da wata cuta ko lokacin da ake gwajin wani sabon magani, wasu kashi 47 cikin dari ne suka yi kuka sakamakon ciwon uwar hanji.

Duk da haka, masu nazarin sun ce, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, LGG na taimakawa wajen sassauta ciwon da jarirai ke fama da shi a uwar hanji, amma yanzu lokaci bai yi ba da za a yi amfani da wadannan kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki, wajen warkar da ciwon uwar jiki kai tsaye.

Ko da yake likitoci sun kwashe shekaru fiye da 50 suna nazarin ciwon da jarirai suke yi a uwar hanji. A daya hannun ba a san ainihin dalilin faruwar ciwon, da kuma illar da ciwon ke haddasawa cikin dogon lokaci ba tukuna. Sa'an nan babu wata hanyar warkar da ciwon.

Nufin jami'ar Turku na gudanar da wannan nazari shi ne kokarin tabbatar da alakar da ke tsakanin ire-iren kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki da ke cikin uwar hanji, da kuma ciwon da jarirai suke yi a uwar hanjin. Sakamakon nazarinsu ya bude wani sabon shafi a fannin yadda za a yi amfani da kananan halittu masu rai kuma masu gina jiki a nan gaba, wajen yin rigakafi da kuma warkar da ciwon da jarirai suka yi a uwar hanji. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China