in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da kasancewar da alaka tsakanin wani maganin kashe kwari da kuma ciwon yara mai nasaba da bugun iska Autism a Turance
2015-07-14 09:17:35 cri

Tun can da, masu nazarin kimiyya sun dade suna shakkar cewa, ko akwai wata alaka a tsakanin batun zama a wurin dake da yawan abubuwa masu guba, da kuma kamuwa da ciwon yara mai nasaba da bugun iska Autism a Turance.

Sai kuma a kwanan baya, wasu masu nazarin kimiyya dake kasar Amurka suka kaddamar da wata makala, inda a cewarsu, idan masu juna biyu suna zama a dab da gonaki, ko makiyaya, ko wuraren shan iska, ko filayen wasan Golf da dai makamantansu, inda ake amfani da maganin kashe kwari, to, barazanar kamuwar jariran su da ciwon yara mai nasaba da bugun iska na karuwa kwarai da gaske ga 'ya'yan dake cikin su.

Masu nazarin daga reshen Davis na jami'ar California ta kasar Amurka, sun kaddamar da makalarsu kan jaridar "sa ido kan muhalli" inda suka bayyana cewa, bayan da suka tantance bayanan tarihin samun jinya kan mutane 970, sun gano cewa, idan masu juna biyu suna zaune a wuraren da ke da nisan da bai wuce kilomita 1.6 daga gonaki, makiyaya da dai sauransu, inda ake amfani da maganin kashe kwari, barazanar da 'ya'yansu ke fuskanta a fannonin kamuwa da ciwon yara mai nasaba da bugun iska, ko kuma matsalar kara girma ba yadda ya kamata ba, ta kan karu da kashi 70 cikin dari sama da sauran mutane.

Har wa yau masu nazarin sun gano cewa, idan masu juna biyu sun shiga makonni 14 zuwa 28 na lokacin samun ciki, ko kuma makonni 28 zuwa 42 na lokacin samun ciki, suna kuma zaune a wuraren da ake yawan amfani da maganin kashe kwari, to, barazanar kamuwa da ciwon yara mai nasaba da bugun iska da 'ya'yansu suke fuskanta ta kan kai matsayin koli.

Alkaluman da cibiyar sarrafa da yin rigakafin cututtuka ta kasar Amurka ta gabatar sun shaida cewa, a shekarun baya da suka wuce, yawan kananan yara da ke fama da ciwon yara mai nasaba da bugun iska na ta karuwa a kasar ta Amurka. A cikin ko wadanne mutane 68, a kan samu mutum guda wanda ke fama da ciwon yara mai nasaba da bugun iska. A wasu wuraren dake da yawan mutane ma dake kasar kuma, adadin ya kan yi matukar haura haka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China