in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalar kiba da iyaye mata ke fuskanta kan kara barazanar mutuwa ga jariransu
2015-08-10 10:36:56 cri

Kwalejin koyon aikin likita na Karolinska dake kasar Sweden ya kaddamar da wani sakamakon sabon nazari a kwanan baya, wanda ke nuna cewa, idan nauyin masu juna biyu ya wuce misali, ko kuma suna fama da matsalar kiba, to jariran da za su haifa za su kara fuskantar barazanar karancin iskar Oxygen. A duk lokacin da nauyin jikin masu juna biyu ke karuwa, sabbin jariran da za su haifa ma za su kara fuskantar wannan barazana.

Masu nazarin sun samu wannan sakamako ne a bincken da suka gudanar kan daukacin jariran da aka haifa daga shekarar 1992 zuwa 2010 a kasar ta Sweden, wannan bai shafi jarirai da dama da aka haife su a lakaci guda ba. Binciken nasu a ta'allaka ne kan jarirai sabbin haihuwa fiye da miliyan 1 da dubu dari 7, inda suka gano cewa,jariran na fuskantar barazanar rashin isasshiyar iska ne yayin da nauyin matan ya wuce misali, ko suna kan sahun masu kiba a lokacin da suka haife su, ko kuma sun zarce rukunin masu madaidaicn nauyi.

Bayanai a kimiyance na nuna cewa, mizanin nauyin mutum a rana ba ya zarce BMI 20,amma idan ya wuce 25, to, nauyin jikin mutum ya wuce misali, yayin da ya wuce 30 kuwa, to hakika mutum ya shiga sahun masu kiba.

Masu nazarin sun gano cewa, idan aka kwatanta nauyin masu juna biyu da ya zo daidai, amma mizanin BMI na daya daga cikinsu ya wuce 25 amma bai kai 30 ba, to barazanar rashin isasshiyar iska da jariransu za su fuskanta cikin mintoci 5 bayan haihuwarsu ta kan karu da kashi 55 cikin dari. Kana kuma idan mizanin BMI na dayan ya wuce 30 amma bai kai 40 ba, to irin wannan barazana ta kan ninka sau 1. Sa'an nan idan mizanin BMI na wata kuma ya wuce 40, to irin wannan barazana kan ninka sau 2.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, mata da dama na fuskantar matsalar kiba yayin da suka samu ciki, don haka yana da muhimmanci matan da suka shirya samun ciki su yi kokarin kauce wa wannan matsala ta nauyin da ya wuce misali ko shiga sahun masu kiba, domin yana da muhimmanci kwarai da gaske ga lafiyan jariran da za su haifa. Amma duk da haka masu nazarin sun ce, ba su fadada nazarinsu kan yadda aka ba da jinya ga jarirai sabbin haihuwa da suka fuskanci rashin isasshiyar iska yayin da aka haife su, da kuma lafiyarsu ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China