in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran cewa ta hanyar nazari kan fitsari za a yi hasashen barazanar haifuwa kafin lokaci
2015-08-16 12:22:03 cri

Jaridar ilimin likitanci ta BMC ta kasar Birtaniya, ta wallafa wani rahoto a 'yan kwanakin baya, wanda ke cewa yawan wasu sinadarai da ke cikin fitsarin masu juna biyu, yana da nasaba da batun haihuwa kafin lokacin da aka yi hasashe, da kuma rashin isasshen nauyin jikin jarirai sabbin haihuwa.

Nan gaba ana sa ran cewa, za a kirkiro wata hanyar bincike, wadda za ta taimaka wajen yin hasashen irin wannan barazana, tare da daukar matakan kandagarkin matsalar cikin lokaci.

Masu nazari da suka fito daga kwalejin koyon kimiyya da fasaha ta kasar Birtaniya, da jami'ar Crete ta kasar Girka sun yi hadin gwiwa wajen tantance yawan sinadaran da ke cikin fitsarin masu juna biyu 438 'yan kasar Girka, wadanda aka tattara fitsarin na su yayin da suka shiga watanni 3 na samun ciki.

Masu nazarin sun gano cewa, a bayyane take, cewa yawan wani nau'in sinadari da ke cikin fitsarin masu juna biyu yana da nasaba da barazanar haifuwa kafin lokacin da aka yi hasashe, yayin da rashin isassun wasu sinadarai da ke cikin fitsarin ya kan hana 'yan tayi su kara girma yadda ya kamata, sa'an hakan na kara wa masu juna biyun barazanar kamuwa da ciwon sukari yayin da suka samu ciki.

Sakamakon nazarce-nazarce da aka gabatar a baya, ya shaida cewa haifuwa kafin lokacin da aka yi hasashe, da kuma matsalar 'yan tayi ta karancin girma yadda ya kamata, kan haifar da barazana da dama ga lafiyar kananan yara. Alal misali, hakan na kara musu barazanar kamuwa da ciwon zuciya bayan da suka balaga.

Kaza lika yin hasashen haifuwa kafin lokacin da aka yi hasashe, da sauran barazana a farkon wa'adin samun ciki, zai taimaka wajen daukar matakai masu nasaba kuma cikin lokaci, tare da ragewa matan masu juna biyu kamuwa da cututtukan dake biyo bayan haihuwa, da matsalolin lafiyar jarirai sabbin haihuwa.

Masu nazarin sun nuna cewa, akwai wata alaka a tsakanin yawan wasu sinadaran da ke cikin fitsarin masu juna biyu a farkon wa'adin samun ciki, da kuma matsalar haifuwa kafin lokacin da aka yi hasashe. Don haka nan gaba ana sa ran cewa, za a iya yin hasashen bullar irin wannan matsala ta hanyar binciken fitsari. Inda masu nazarin za su fadada binciken su, domin tabbatar da sakamakon wannan nazari. Duk dai da cewa akwai lokaci mai tsayi, kafin cikar burin na su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China