in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana iya gadar tsoro daga zuriya zuwa zuriya
2015-07-06 16:29:50 cri

Masu karatu, ko kun san cewa ana iya gadar tsoro daga zuriya zuwa zuriya tsakanin dabbobi da mu 'yan Adam?

Wani sabon nazari da aka yi kan dabbobi a kasar Amurka, ya shaida cewa beraye jarirai sabbin haihuwa, su kan koyi abubuwan da kamata sub a su tsoro, ta hanyar sansanar warin da iyayensu mata suke fitarwa yayin da suka ji tsoro.

An kaddamar da sakamakon nazarin a jaridar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Amurka wato PNAS. Masu nazari daga jami'ar Michigan wadanda suka gudanar da nazarin sun bayyana cewa, nazarinsu ya shaida cewa, jarirai sabbin haihuwa na iya koyon abubuwan da suke tsorata iyayensu mata. Kuma batun da ya fi muhimmanci shi ne jariran ba sa mantawa da abubuwan da suka rike masu ban tsro daga iyayensu mata cikin kwakwalwar su, sabanin wasu abubuwan na daban wadanda idan ba su maimaita su ba, su ke iya mantawa da su a sauran hanyoyi a lokacin da suke matsayin jarirai.

Masu nazari daga jami'ar Michigan da jami'ar New York sun horas da beraye mata jin tsoron kamshin ganyen na'ana'a. Da farko, da zarar beraye mata sun shaki kamshin na'ana'a, sai sanya musu lantarki a jin su, ta haka berayen suka hada kamshin na'ana'a da kuma ciwon da suke ji sakamakon lantarki da yake kama su. Daga nan sai masu nazarin suka sanya wadannan beraye samun juna biyu, suka bar su da kuma jariransu sabbin haihuwa a wani wuri mai cike da kamshin na'ana'a, amma ba a sa musu lantarki a jiki.

Masu nazarin sun gano cewa, kamshin na'ana'ar ya na tada hankalin wadannan beraye iyaye mata, ya sa suji tsoron kamshin na'anar, sa'an nan a lokaci guda yana ta da hankalin jariransu.

To ko ina dalilin da ya sa haka? Masu nazarin sun gano cewa, beraye jariran sukan shaki kamshin na'ana'ar da kuma warin da iyayensu mata suke fitarwa yayin da tsoro ke kama su. Kuma ko da iyayen na su mata ba su nuna wata alama ba, berayen jariran sukan yi koyi daga wajensu, su ji tsoron kamshin na'ana'ar kamar yadda iyayensu mata suke yi, hakan ya nuna cewa, beraye iyaye mata sun koyar da tsoro ga jariransu ta hanyar fitar da warin musamman yayin da suke jin tsoro. Wanda hakan ke nuna cewa ana iya gadar tsoro daga zuriya zuwa zuriya.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, idan mata sun ji rauni a tunaninsu kafin su samu ciki, hakan zai yi mummunar illa ga jariransu.

Don haka sabon nazarin da aka yi zai taimaka wajen gano dalilin da ya sa hakan, kuma zai iya bada damar lalubo bakin zaren warware wannan matsala. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China