in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu a ko wace rana na da amfani ga lafiyar kwakwalwa da zuciyar dan Adam
2015-06-08 17:37:00 cri


Wani nazarin da aka shafe dogon lokaci ana gudanarwa a kasar Japan, ya shaida cewa tabbas yawan cin kayayyakin lambu, da 'ya'yan itatuwa, na iya rage barazanar mutuwar dan Adam, sakamakon kamuwa da shan inna a kwakwalwa, da kuma ciwon zuciya. Don haka masu nazarin suka ba da shawarar cewa, ya fi kyau a ci kayayyakin lambu, da 'ya'yan itatuwa a ko wace rana.

Jami'ar kimiyya da fasaha ta nazarin lafiyar jikin dan Adam a kasar Japan, ta kaddamar da wani rahoton nazari a kwanan baya, inda ta ce wata tawagar nazari daga jami'ar ta zabi Japanawa 9112, daga sassa daban daban na kasar cikin wadanda suka taba shiga nazarin da aka gudanar a shekarar 1980, dangane da yadda mutanen kasar ke cin abubuwa masu gina lafiyar jiki.

Dukkanin wadannan mutane 9112 shekarunsu sun wuce 30 amma basu kai 80 a duniya ba, a lokacin da aka yi bincike kan su a shekarar 1980, kuma ba su taba kamuwa da shan inna a kwakwalwarsu, ko toshewar jijiyar jini a zuciyarsu ba. Masu nazarin sun kwashe shekaru 24 suna gudanar da nazarin, wato daga shekarar 1980 zuwa 2004.

A cikin wadannan shekaru 24 da suka gabata, wasu daga cikin mutane 831 sun rasu ne sakamakon kamuwa da shan inna a kwakwalwarsu, da toshewar jijiyar jini a zuciyarsu, da sauran cututtukan kayayyakin ciki masu taimakawa gudanar jini. Masu nazarin sun gano cewa, idan an kwatanta wadanda su kan ci kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa, da yawansu ya kai giram 486 a ko wace rana, da kuma wadanda su kan ci kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da yawansu ya kai giram 275 a ko wace rana, lallai barazanar mutuwa da wadanda suka fi cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa a ko wace rana suke fuskanta, sakamakon kamuwa da cututtukan kayayyakin ciki masu taimakawa gudanar jini, ta ragu da kashi 28 cikin dari.

Har wa yau kuma, masu nazarin sun gano cewa, wadanda kan ci kayayyakin lambu kawai a ko wace rana, ko masu cin 'ya'yan itatuwa kawai a ko wace rana, barazanar mutuwa da suke fuskanta sakamakon kamuwa da cututtukan kayayyakin ciki masu taimakawa gudanar jini na kara raguwa matuka sabanin wadanda ba sa yin hakan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China