in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a yi kandagarkin ciwon kansar fata tun daga yarinta
2015-05-10 14:42:19 cri


Kwanan baya, ma'aikatar kula da harkokin muhalli ta kasar Jamus, ta yi gargadin cewa, kunar-rana a jiki a lokacin yarinta, wani muhimmin dalili ne da ke haddasa saurin kamuwa da ciwon kansar fata. Don haka kamata ya yi a yi kandagarkin kamuwa da ciwon kansar fata, ta hanyar kare kananan yara daga yawan hasken rana.

Ma'aikatar kula da harkokin muhalli ta Jamus din ta ce, bai kamata a kau da kai daga kare kananan yara daga hasken rana ba. Kuma ya zama tilas iyaye su sauke nauyin dake kan su a wannan fanni, musamman ma a lokacin hutu. Dole ne iyaye su kare yaransu daga yawan hasken rana.

Ta ce yaran da suka yi yini guda suna wasa a rairayin bakin teku, ko kuma a bankin tabki, mai yiwuwa ne su samu kunar rana a jikinsu, lamarin da ka iya zai zama dalilin kamuwa da ciwon kansar fata a nan gaba.

To idan haka ne ta yaya za a kare yara daga yawan hasken rana yadda ya kamata?

Amsa a nan ita ce ya zama wajibi baligai su kara mai da hankali wajen kare yara daga hasken rana. Ma'aikatar kula da harkokin muhalli ta Jamus ta gabatar wa makarantu, da makarantun renon yara littattafan koyarwa na kare yara daga yawan hasken rana, tare da inganta horas da malamai.

Har wa yau ma'aikatar ta kaddamar da jerin abubuwan da ya kamata a lura da su, a fannin kare yara daga yawan hasken rana, don mutane su koya.

Da farko dai, akwai batun sanya tufafi yadda ya kamata. Wato ya fi kyau a sanya tufafi maras kama jiki, kamar T-shirt, da wando ko siket da ya wuce gwiwa, sa'an nan a sanya takalma, da babbar hula ko kuma kalluban da ke iya kare wuya.

Na biyu kuma a sanya tabarau yaddda ya kamata, a kokarin kiyaye idanun yara. Dole ne a sayi takarau da ke iya yaki da hasken Ultraviolet Rays (wato nau'in hasken rana mai illa ga fatar jiki), kuma ya kamata launin tabarau din, ya zamo launin toka-toka ne, ko kuma mai launin kasa-kasa ne.

Na uku a shafa wa yara isashen man ba da kariya daga hasken rana a fatan su kafin su fita waje, sa'an nan a kara shafawa yara in akwai bukata. Kamata ya yi a shafa man ba da kariya daga hasken rana na UVB da UVA duka.

Na hudu kuma a yi kokarin gujewa hasken rana daga karfe 11 na safe zuwa karfe 3 na yamma, saboda a wannan tsawon lokaci ne hasken Ultraviolet Rays ya fi tsanani. Har wa yau ya fi kyau a kasance a karkashin inuwa ko kuma cikin dakuna, hakan zai sanya yara su dan ji sanyi kuma ya kare su daga samun kunar rana a jiki.

Na biyar kuwa, kada a manta da shan ruwa! Yin gumi kan kone ruwan jikin yara, don haka ya zama tilas a maido da ruwan ta hanyar shan wani. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China