in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara ci ko shan sinadarin Iron yana taimakawa wajen rage barazanar fuskantar larurorin da mata ke fuskanta kafin zuwan al'adarsu
2015-05-18 07:18:23 cri


Mata masu yawa kan yi saurin fushi ko mutsu-mutsu, ko juyayi, ko kuma su rika jin ciwo a mamansu, lamarin da ake kira "larurori da mata ke fuskanta kafin zuwa al'adarsu" wato PMS a Turance.

Game da wannan larura wani nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya shaida cewa, idan an dan kara madaidaicin sinadarin Iron a cikin abinci, hakan zai taimakawa mata rage yiwuwar samun wannan matsala ta ciwon PMS.

Wata kungiyar nazari daga reshen jami'ar Massachusetts a Amherst ta kasar Amurka, ta kwashe shekaru 10 tana tantance masu aikin jiyya mata dubu 3 da 25, wadanda shekarunsu ke tsakanin 25 zuwa 42 a duniya. Sun baiwa wadannan mata takardun tambaya dangane da yawan abinci, da sinadarai iri iri guda 131 da suke ci ko sha. Wadannan masu aikin jiyya ba sa yin fama da ciwon PMS kafin a sanya su cikin binciken. Amma a lokacin da ake gudanar da nazarin, wasu dubu 1 da 57 daga cikinsu sun fara fama da ciwon.

Bayan da aka kwatanta abincin da wadannan masu aikin jiyya dubu 1 da 57, da sauran masu aikin jiyya su kan ci, masu nazarin sun gano cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, in an kwatanta wadanda su kan ci sinadarin Iron mai nauyin milligram 10 a ko wace rana, yiwuwar kamuwa da ciwon PMS da wadanda su kan ci sinadarin mai nauyin milligram 22 a ko wace rana suke fuskanta, ya ragu da kashi 33 cikin dari. Don haka yawan sinadarin na Iron da cibiyar nazarin magunguna ta Amurka ta ba da shawarar a ci a ko wace rana shi ne milligram 18.

Sai dai duk da cew kara yawan sinadarin karfe da mata kan ci a ko wace rana na kara rage yiwuwar kamuwa da ciwon PMS, a hannu guda a kokarin magance abkuwar sakamako maras kyau bisa hakan, masu nazarin sun shawarci mata da su ci sinadarin na Iron dai-wa-dai da, kana kuma bai kamata a ci sinadarin na Iron ko wani nau'in sinadari shi kadai ba, wato kamata ya yi a ci abinci iri daban daban da zai samar da sinadarin.

Haka zalika masu nazarin sun yi nuni da cewa, a baya, binciken da aka yi sun mai da hankali kan yadda za a warkar da ciwon PMS, da kuma gano dalilan da suke haifar da ciwon. Amma nazarin da aka yi a wannan karo ya juya hankali kan alakar da ke tsakanin cin wasu sinadarai da ciwon PMS, koda yake nazarin bai tabbatar da cewa, sinadarin na Iron na iya yin rigakafin ciwon PMS ba.

Kididdiga ta shaida cewa, Amurkawa mata da yawansu ya kai kashi 8 zuwa 15 cikin dari ne suke fama da ciwon PMS.

An kaddamar da sakamakon nazarin a cikin mujallar "ilmin cututtuka masu yaduwa" ta Amurka. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China