in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban matsin lamba ta fuskar aiki ka iya sanya mutane kamuwa da ciwon sukari
2015-05-02 19:43:59 cri


Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Jamus, ya yi gargadin cewa, mai yiwuwa mutanen da ke fuskantar babban matsin lamba ta fuskar aiki, kuma ba su mai da hankali kan sarrafa gudanar aiki sosai, su fi fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari da kashi 63 cikin dari, in an kwatanta da sauran mutane.

Kafofin yada labaru na kasar Jamus sun labarta ewa a kwanan baya, masu nazari daga jami'ar masana'antu ta Munich dake kasar, sun kwashe shekaru 12 suna tantance lafiyar mutane fiye da dubu 5.

A farkon lokacin gudanar da nazarin, dukkan wadannan mutane ba su kamu da ciwon sukari ba, dukkansu kuma sun cike takardun tambaya dangane da ayyukansu, da yadda suka sauke nauyinsu na ayyuka, da matsayin kwarewarsu a fannin gudanar da aiki da dai sauransu.

Bisa amsoshinsu ne masu nazarin suka tantance wadanda suke fuskantar matsin lamba ta fuskar aiki, ko wadanda suke gudanar da aikinsu bisa dacewa cikin daukacin mutanen.

A cikin wadannan shekaru 12, kimanin mutane dari 3 sun kamu da ciwon sukari, a cikinsu kuma kashi 7 cikin dari ne suke fuskantar babban matsin lamba ta fuskar aiki. Kana kuma yawan mutanen da ba su sarrafa gudanar aiki sosai, wadanda suka kamu da ciwon sukari shi ma ya yi yawa.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, mutanen da suke fuskantar babban matsin lamba ta fuskar aiki su kan gamu da matsaloki a al'adar zaman rayuwarsu, kamar shan taba, ko shan giya, ko rashin cin abinci yadda ya kamata, matakan da dukkansu za su iya sanyawa mutane su kamu da ciwon sukari.

Har wa yau kuma, matsin lamba ta fuskar aiki kan haifar da rashin daidaiton wasu sinadarai a jikinin mutane, ta yadda mutane ba za su iya sarrafa yawan sukarin da ke jikinsu yadda ya kamata ba.

A baya wasu nazari sun yi mana kashedi da cewa, babban matsin lamba ta fuskar aiki, kan kara barazanar abkuwar ciwon zuciya da kuma mutuwar mutane. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China