in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawancin mutane sun raina barazanar da ciwon sukari kan haddasa ga lafiyarsu
2015-03-09 13:59:44 cri


Ko da yake ciwon sukari yana yiwa lafiyar karin mutane barazana, amma wani sabon nazarin da aka yi a kasar Birtaniya ya nuna mana cewa, ya zuwa yanzu yawancin mutane ba su san barazanar da mai yiwuwa wannan ciwo zai haifar ga lafiyarsu ba. Kwararru sun bayyana cewa, ilmantar da mutane kan ciwon sukari yana iya taimakawa wajen rage wannan barazana.

Wata kungiya da ke taimakawa masu fama da ciwon Sukari mai suna "Birtaniya da ciwon sukari" ta fito da wani rahoto a kwanakin baya cewa, kungiyar ta yi bincike kan 'yan Birtaniya dubu 1 dangane da ciwon sukari nau'I na II, inda ta gano cewa, yawancin wadannan mutane sun raina barazanar da ciwon sukari ke haddasawa. Alal misali, kashi 30 cikin dari daga cikinsu na sane da cewa, mai yiwuwa ne ciwon sukari zai sanya mutane su kamu da ciwon ido, har ma su makance, yayin da kashi 13 cikin dari ne kawai suke da masaniyar cewa, watakila ciwon sukari zai sa mutane su kamu da ciwon zuciya, kana kashi 7 cikin dari ne kawai suka san cewa, watakila ciwon sukari zai sanya mutane su kamu da shanyewar jiki. Kungiyar ta yi hasashen cewa, a shekarar 2025, 'yan Birtaniya kimanin miliyan 5 ne za su kamu da ciwon sukari nau'I na II wato type 2 a turance, adadin da zai ninka har sau daya bisa na shekarar 2008, don haka Birtaniya za ta fuskanci karin matsin lamba wajen ba da hidimomin kiwon lafiya.

Masu nazari daga kungiyar kuma sun bayyana cewa, a ko wace shekara mutane kimanin dubu 70 ne ke mutuwa sakamakon ciwon sukari nau'I na II ko cututtukan da suka bijiro sanadiyar ciwon sukarin a Birtaniya. Ko da yake kara cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa, motsa jiki yadda ya kamata da tabbatar da nauyin jikin da ya dace suna iya hana yawancin masu fama da ciwon sukarin kamuwa da wani ciwon.

Bayan haka kuma, kungiyar ta "Birtaniya da ciwon sukari" ta kaddamar da wani aikin fadakar da mutane game da ciwon sukari a duk fadin Birtaniya. Masu nazarin daga kungiyar sun yi nuni da cewa, yin rayuwa mai kyau na iya ragewa mutum yiwuwar kamuwa da ciwon sukari da kuma barazanar mutuwa sakamakon ciwon. Amma mutane masu dimbin yawa ba su san da haka ba, don haka aikin ilmantar da mutane game da wannan ciwo na da matukar muhimmanci. Har ila yau kuma fadakar da mutane kan binciken hawan jini kullum na da amfani wajen rage barazanar kamuwa da cututtukan da ke da nasaba da zuciya da na magudanar jini da ke da nasaba da ciwon sukari. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China