in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin cakulan kadan na iya rage barazanar shanyewar jiki
2014-12-28 15:03:43 cri

Bai kamata wadanda ba sa kaunar yin kiba su rika cin Cakulan ba. Domin yawan cin cakulan fiye da kima kan sanya mutane su yi kiba. Amma duk da haka kwalejin nazarin ilmin likitanci na Royal Caroline na kasar Sweden ya gabatar da sakamakon nazarinsa a kwanan baya cewa, cin rika cin cakulan kadan a ko wace rana na iya taimakawa wajen rage barazanar shanyewar jiki.

Masu nazari daga kwalejin nazarin ilmin likitanci na Royal Caroline na kasar Sweden sun yi gudanar da nazarinsu ne kan 'yan kasar maza fiye da dubu 37 wadanda shekarunsu suka wuce 49 amma ba su zarta 75 a duniya ba. Bayanan lafiyar wadannan mazaje sun shaida cewa, a cikin shekaru 10, wasu daga cikinsu kusan dubu 2 sun gamu da shanyewar jiki. Masu nazarin sun yi musu tambayoyi a rubuce kan yadda suke cin abinci, ciki had da yawan cakulan da su kan ci.

Masu nazarin sun gano cewa, a cikin dukkan mazan da suka gudanar da bincike a kansu, barazanar gamuwa da shanyewar jiki ga wadanda suka ci cakulan kadan ne sannan wadanda ba su ci cakulan din ba ta dara wadanda su kan ci cakulan da yawa. Barazanar gamuwa da shanyewar jiki ta ragu da kashi 17 cikin dari sakamakon cin cakulan da ya kai gram 63 a ko wane mako.

A kokarin kara tabbatar da amfanin cakulan, masu nazarin sun tantance bayanan da suka samu da kuma bayanan da aka samu a nazarce-nazarce guda 4 da aka yi a baya a sauran kasashe, ciki hada da wani nazari kusan iri daya da aka yi a shekarar 2011, inda aka yi nazari kan mata. Sakamakon dukkan nazarce-nazarce guda 5 din da aka yi sun kusa zama daidai da juna.

Dangane da amfanin cakulan a fannin rage barazanar gamuwa da shanyewar jiki, masu nazarin sun cewa, ana bukatar gudanar da karin nazari domin kara sanin dalilin da ya sa ake samun wannan sako. Amma suna ganin cewa, watakila sinadaran da ke cikin cakulan ne suke taka wannan rawa, wadanda kuma ake samunsu a cikin ganyayen shayi, giya, albasa da tuffa.

Amma duk da haka masu nazarin sun bayyana cewa, sakamakon nazarinsu ba ya nuna cewa, cin cakulan kawai zai iya kare mutane daga gamuwa da matsalar ta shanyewar jiki. Cin cakulan mai yawa fiye da kima na kara nauyin jikin da zai kai ga kiba, wadda hakan kan haddasa sauran matsalolin lafiya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China