in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai saurin fushi kan iya kamuwa da shanyewar jiki cikin sauki
2015-01-11 15:17:58 cri


Sinawa kan ce, yin dariya yana tsawaita ran mutum da shekaru 10. Amma idan mutum ya cika yin saurin fushi fa?

Wani sabon nazari ya yi gargadi da cewa, mai saurin fushi kan iya kara fuskantar barazanar kamuwa da shanyewar jiki, hakan ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin farin ciki ga lafiyar dan Adam.

Wani rahoton bincike da wasu masu nazari daga kasar Spain suka gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, sun yi bincike kan lafiyar masu fama da shanyewar jiki 150, wadanda shekarunsu suka wuce 18 amma ba su wuce 65 a duniya ba, matsakaicin shekarunsu ya kai 53.8 da haihuwa. Sun kuma tantance su da wasu mutane dari 3 da ke zaune a wuri guda.

Sakamakon tantancewar ya bayyana cewa, mutanen da suka fi saurin fusata, da son yin gogayya, da gajan hakuri sun fi fuskantar ninkin barazanar kamuwa da shanyewar jiki ko fiye da haka.

Wannan nazari ya bayyana alakar da ke tsakanin matsalar saurin fushi da barazanar kamuwa da shanyewar jiki, amma watakila akwai wani dalilin da ya sa hakan ke faruwa a cikin jikin mutane. A kullum mutanen da suka fi saurin fusata, da son yin gogayya, da gajan hakuri kan fuskanci babban matsin lamba, wadda hakan kan tayar da hawan jini. Sanin Kowa ne cewa, hawan jini, shi ke haifar da shanyewar jiki.

Amma duk da haka masu nazarin na ganin cewa, nazarin da suka yi ya shafi wasu 'yan kasar Spain ne da ke zaune a birnin Madrid, babban birnin kasar kawai. Mai yiwuwa ne sakamakon nazarin nasu ba zai dace da mutanen da ke zaune a sauran wurare ba.

Ban da haka kuma, wannan nazarin da masu nazarin Spain suka yi ya tabbatar da wasu dalilan da suka haddasa karuwar barazanar shanyewar jiki, wadanda a baya aka san su, kamar shan taba, shan giya fiye da kima, rashin yin barci yadda ya kamata, dukkansu suna kara wa mutane barazanar kamuwa da shanyewar jiki.

Sabili da haka ne ma, masu nazarin suka ba da shawarar cewa, hanya mafi dacewa da ya kamata mutane su bi wajen rage barazanar kamuwa da shanyewar jiki ita ce, cin abinci da likitoci suka amince da su, kara motsa jiki, daina shan taba, yin kokarin kaucewa shan giya, da yin rayuwa ta hanyar da ta dace. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China