in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bambancin lokacin da masu juna biyu ke dauka kafin haihuwa na iya kaiwa makonni 5
2015-02-16 15:18:00 cri


A yawancin lokuta, akan ce mata masu juna biyu na shafe watanni 10 kafin su haihu. Amma sakamakon wani sabon bincike ya nuna cewa tazara tsakanin haihuwar mata masu juna na iya kaiwa har makwanni 5.
Binciken da mujallar Human Reproduction mai fidda bayanai kan nazarin haihuwar dan Adam ta kasar Birtaniya ta wallafi, ya nuna cewa nazarin da aka yi a kwanan baya a kasar Amurka, ya nuna cewa yawacin lokaci, ana hasashen haihuwar jarirai ne bayan kwanaki 280, bayan zuwanal'adar iyaye mata na karshe, sai dai alal hakika cikin adadin mata masu juna, kusan kashi 4 cikin dari ne kawai suke haifar jariransu a daidai lokacin haihuwar da aka yi hasashe, yayin da wasu kashi 70 cikin dari daga cikinsu kan haihu cikin kwanaki 10 kafin, ko bayan lokacin haihuwar da aka yi hasashe.
Kwalejin nazarin kimiyyar muhalli da kiwon lafiya ta kasar Amurka ta yi nazari kan masu juna biyu su 125, inda bayan da masu nazarin suka tantance daidai lokacin da suka samu ciki, da kuma daidai lokacin haihuwar su, sun gano cewa tsawon lokacin da suka samu juna biyu ya kai makonni 35 zuwa 40 da rabi, sakamakon da ya nuna yadda suka sha bamban sosai da juna.
Sai dai wannan nazari bai shafi masu juna biyu da suka haihu kafin lokacin da aka yi hasashe ba. Matan da aka yi musu binciken sun haihu yadda ya kamata.
Har wa yau masu nazarin sun gano cewa, tsahon lokacin da masu juna biyu suke yi da ciki, yana da nasaba da halin da suke ciki. Alal misali, ga matan da suka dan girma, wa'adin cikin su ya kan fi tsawo. Ya yin da kuma matan da nauyin jikin su ke da yawa a lokacin da aka haife su kuma, lokacin da suke da ciki ya kan fi tsawo. Haka kuma, idan mace ta shafe tsahon lokaci da ciki, haihuwar ta a ciki na gaba ma na iya yin tsawo.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, lokacin da mata suke da ciki ya sha bamban da juna sosai, bambancin lokacin da ka iya kaiwa makonni 5. Don haka yayin da likitoci suke hasashe kan lokacin haihuwa, kamata ya yi su yi la'akari da bambancin da ke tsakanin matan. (Tasallah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China