in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki da masu aikata laifukan cin amanar kasa a kasar Sin
2014-07-03 09:43:51 cri

Wannan muhimmin mataki da shugabannin jam'iyar kwaminist karkashin jagorancin shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping suke aiwatarwa a zahiri ga masu aikata laifikan cin amanar kasa a kasar Sin, babban batu ne da shugabannin kasar Sin ke sa mahimmanci akai. Babu shakka, matakan da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa na yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasar Sin, zai taimaka sosai wajen kawar da aiyukan cin amanar kasa a kasar Sin kana zai kara tsabtace yanayin gudanarwar jam'iyar kwaminist ta kasar Sin tare da kara kwarjini da kima da tagomashin kasar Sin a idanun al'ummar Sinawa da ma kara kare martaba da kimar kasar Sin a idanun al'ummomin duniya baki daya. Matakin ba shina, ba sabo da sabbin shugabannin kasar Sin suka fara aiwatarwa tun a shekarar bara ta 2013 kawo yanzu shekarar 2014, ya alamunta damuwar da shugabannin kasar Sin karkashin jagorancin shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping ke nunawa na kawar da aiyukan cin amanar kasa a kasar Sin. Ko a ranar lahadi 22 ga watan 09 shekarar bara ta 2013 ma, sai da wata kotun al'umma dake zamanta a garin Jinin na lardin Shandong dake arewa maso yammacin kasar Sin suka yanke hukuncin daurin rai da rai akan Bo Xilai wanda kafin hukuncin jigo ne kuma mai rike da babban mukami a jam'iyar kwaminist ta kasar Sin. Dan haka, wannan matakin korar tsohon mataimakin shugaban rundunar sojojin kasar Sin Xu Caihou daga cikin jam'iyar kwaminist tare da mika shi ga hukumar bunciken laifuka ta rundunar sojojin kasar Sin, wani muhimmin mataki ne na kawar da masu aikata laifukan cin hanci da karbar rashawa a kasar Sin. Muna fata mu ma wata rana a kasashenmu na Afirka shugabanni za su hanzarta yin koyi da shugabannin kasar Sin wajen dakile yaduwar dabi'ar cin amanar kasa a Afirka.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China