in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a yi makara ba idan wani ya fara motsa jiki yayin da shekarunsa ya kai 50 a duniya
2014-06-23 09:20:23 cri

Assalamu Alaikun, jama'a masu sauraro. Sashen Hausa na rediyon kasar Sin CRI ke gabatar muku da shirin "Lafiya Uwar Jiki". Kuma ni ce Tasallah ke muku marhabin a wannan zaure daga nan birnin Beijing, inda zan gabatar muku wasu muhimman bayanai game da yadda za mu kara kula da lafiyarmu yadda ya kamata. (music)

Wasu mutane na tsammanin cewa, ya kamata a motsa jiki da yawa a lokacin kuruciya. Idan mutum ya tsufa, watakila motsa jiki ba zai yi masa ba. Amma wani bincike da masu nazari na kasar Birtaniya suka yi ya nuna cewa, ko da mutum ya fara motsa jikinsa yayin da shekarunsa suka kai 50 a duniya, kuma ya kan motsa jikinsa ba tare da kasala ba, to, lafiyarsa ta kan fi ta wadanda ba safai su kan motsa jiki ba a wasu fannoni.

Kwanan baya, wasu nazari daga hukumomi da kwalejoji na kasar Birtaniya sun rubuta wani rahoto a wata mujallar kimiya inda su ke cewa, sun yi shekaru 10 suna gudanar da wani bincike kan tsoffafi da masu matsakacin shekaru fiye da dubu 4, wadanda matsakacin shekarunsu ya kai 49 a duniya a yayin da aka kaddamar da wannan bincike.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, kusan rabin wadannan mutane su kan motsa jiki yadda ya kamata na tsawon awa 2 da rabi a ko wane mako, hakan ya taimaka ga koshin lafiyarsu. Su kan yi gudu ko su yi wasa da kwallo ko motsa jiki ta wasu hanyoyi, ta yadda saurin bugun zuciyarsu ya karu kuma watakila su kan yi gumi yayin da suke motsa jikin nasu.

Masu nazarin sun yi nazari kan ma'aunan lafiyar wadannan mutane. In an kwatanta su da wadanda ba safai su kan motsa jiki ba, abubuwan da ke da nasaba da kamuwa da ciwon zuciya da ke cikin jikin wadanda su kan motsa jiki yadda ya kamata ba su da yawa sam. Ciwon zuciya wani irin ciwo ne da tsoffafi kan yi fama da shi. Don haka ma iya cewa, mutanen da su kan motsa jikinsu ba tare da kasala ba su kan kasance cikin koshin lafiya.

A baya an taba gudanar da bincike na gajeren lokaci kan yadda motsa jiki yake taimakawa lafiyar zuciya. Amma binciken da masu nazari na Birtaniya suka yi ya dauki tsawon shekaru 10 ne baki daya, wanda ya tabbatar da tasirin da motsa jiki ke da shi ga mutane. Haka kuma ko da shekarun mutum ya wuce 50 a duniya, zai iya cin gajiyar motsa jiki yadda ya kamata. Idan bayan da mutum ya yi ritaya daga aiki, ya mai da hankali kan motsa jiki a lokacin hutunsa, to, zai iya kasancewa cikin koshin lafiya.

To, masu sauraro, da wannan muka kawo karshen shirinmu na yau na "Lafiya Uwar Jiki", inda muka kawo maku muhimman bayanai da ke cewa, Ba a makara ba idan mutum ya fara motsa jiki yayin da shekarunsa ya kai 50 a duniya, da fatan an amfana da sauraronmu. Ni ce Tasallah ke fatan ku kasance lafiya daga nan sashen Hausa na CRI a Beijing.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China