in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matan Sinawa a birnin Sanya suna taka rawar gani ta fannin bunkasa tattalin arziki
2013-09-07 15:24:08 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na saurari shirinku na 'In ba ku' na ranar Litinin 2 ga wata, wanda Malama Bilkisu (Xin Yuhui) ta gabatar mana dangane da kyakkyawar rawar da matan Musulmi 'yan kabilar Hui dake birnin Sanya na kudancin kasar Sin ke takawa ta fannin raya tattalin arzikin birnin.

Hakika, wannan shiri ya burge ni saboda yadda muka saurari rahoton wakilan CRI da suka ziyarci garin suka dauko dangane da yadda matan kabilar Hui ke ba da gagarumar gudunmawa wajen raya tattalin arzikin birnin Sanya. Ba zan manta da hirar da aka yi da wasu mata biyu 'yan kabilar ta Hui ba cikin shirin inda kowacce ta bayyana yadda ta fara kasuwanci sannu-sannu kafin daga bisani harkar kasuwancinta ya samu habaka. Ga misali, Madam Liu Shahua dake kantin sayar da kayan da aka saka, ta bayyana yadda jarin kasuwancinta ya habaka. Haka nan, Madam Ha Yomei dake sayar da lu'ulu'u ita ta bayyana yadda nata kasuwancin ya samu ci gaba.

Wato, abin da ya fi burge ni da wannan rahoto shi ne cewa wadannan mata biyu da wakilan CRI suka zanta dasu kadan ne daga cikin mata da yawa dake gudanar da harkokin kasuwanci a birnin na Sanya, lamarin dake nuna irin babban sauyin da aka samu ta fannin kasuwancin mata a kasar Sin idan an kwatanta da kafin shekarar 1978 lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida tare da bude kofofinta ga kasashen waje.

Lalle, yanzu akwai wata kyakkyawar shaida dake tabbatar da ci gaban tattalin arziki da matan Musulmi 'yan kabilar Hui dake birnin Sanya na kudancin kasar Sin suka samu, sakamakon yadda alkaluman kididdiga suka nuna cewa matan garin ne ke rike da kashi 50 cikin 100 na tattalin arziki. Hakika, wannan ba zai zama wani abin mamaki ba idan an yi la'akari da shigar matan kabilar ta Hui cikin harkokin kasuwanci dake da tasiri kamar mallakar dakunan cin abinci game da gina dakunan kwanan baki har 28 da dai sauransu. Ba shakka, wanann ya zama wani kalubale ga matan nahiyar Afirka wajen shiga kowacce harkar kasuwanci domin a dama dasu, a maimakon yadda mafi yawa daga cikinsu ke ci gaba da dogaro dari bisa dari ga mazajensu, lamarin da a koda yaushe ke haddasa sabani tsakanin ma'aurata.

A karshe, ina yi muku godiya bisa kawo mana wannan shiri mai dadi tare da debe kewa musamman yadda a karshen shirin ku ka sanya mana waka mai dadin ji mai taken "'yan matan kabilar Hui". Na gode.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

birnin Kano, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China