in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina goyon bayan matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka domin dakile matsalar cin hanci da karbar rashawa
2013-09-01 16:55:27 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, jiya Jumu'a 23 ga watan Agusta cikin shirinku na labarai na saurari wani labarai da ya ja hankali na sosai. Wato labarin ci gaba da shari'ar tsohon jami'in gwamnatin kasar Sin, Bo Xilai a wata kotun birnin Jinan dangane da zarge-zargen da ake yi masa dangane da karbar cin hanci da rashawa, da yin almubazzaranci da dukiyar al'umma game da amfani da mukaminsa ba ta hyanyar da ta dace ba.

Hakika, wannan labari ba ma kawai burge ni yayi ba, ya kuma ja hankali na sosai, har nake fatan wata rana a samu irin wannan ci gaba ta fuskar gudanar da harkokin shari'a a nahiyarmu ta Afirka wajen nuna halin 'ba sani ba sabo' ga manyan jami'an gwamnati dake yi wa doka hawan kawara. Saboda wannan shari'a ta Bo Xilai ta zama wata ishara ko darasi ga sauran jami'an gwamnatin kasar Sin manya da kanana, kuma wannan ya nuna cewa da gaske sababbin shugabanni a kasar Sin karkashin JKS suke yi wajen fatattakar wannan mummunar dabi'a ta karbar na goro da masu rike da mukaman gwamnati ke yi. Dangane da haka, ina matukar goyon bayan matakan da hukumomin kasar Sin ke dauka na gurfanar da bmanyan jami'ai dake aikata manyan laifuka da ka iya haddasa koma bayan tattalin arziki da ci gaban kasa. Ko shakka babu, idan kasar Sin ba ta daukan irin wadannan kwararan matakai na yaki da matsalar cin hanci da karbare rashawa, da ba zata samu matsayin da take kai a halin yanzu ba na kasancewa kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya.

Dangane da haka, yan kamata ko ma nace ya zama wajibi kasashen mu na Afirka su yi koyi da kasar Sin wajen yin dirar mikiya kan gurbatattun jami'an gwamnati ko mu ma mun samu ci gaban tattalin arziki. Saboda nahiyar tamu ta Afirka ta kunshi wasu daga cikin kasashen dake kan gaba wajen batun karbar na goro ko toshiyar baki a duk duniya, lamarin da koda yaushe ke mayar da hannun agogo baya ga batun ci gaban nahiyar, musamman idan aka dubi yadda matsalar ke ci gaba da habaka tare da taimaka wa wasu shugabannin nahiyar damar zama 'yan kama karya tare da dauwama kan madafun iko. Don haka, ya kamata shugabanni a Afirka su sake tunani, saboda idan har ba a kawar da matsalar cin hanci da karbar rashawa ba to ba zamu taba samun ci gaba, sai dai na mai hakar rijiya. Bahaushe dai yace, "kukan kurciya jawabine.........."

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon-Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China