Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kunanan lafiya.
Bayan ina farin cikin sanar muku da jin dadin shirinku na sin da Afirka na ranar Talatar data wuce wanda kuka maimata jiya akan hirar da kukayi da Malam Abubakar Haruna Gwammaja wanda ake gaiyata domin bikin karamar Sallah a kasar Sin, gaskiya wannan shiri ya kayatar dani domin ganin cewa Malam Abubakar a kusa dani yani domin ina zaunene a unguwar Kofar Mazugal inda kusan a hade take da unguwar Gwammaja, wannan shiri yakaramin kwarin gwiwa.
Haka kuma ranar 14 -8-13 shirin gani ya koriji akan aikinyi da dalibai sukeyi na wucin gadi bayan sun sami dama a kasar Sin a gaskiya na karu sosai a matsayin wanda yake da niyyar karo karatu a wasu kasashe, wanda a yanzu zan iya bawa dalibai shawarar yadda zasu tserewa yan damfara masu zaluntansu wajen samar masu da aikinyi.
Ina muku fatan alheri.
Zai Jian, Xie Xieni.
Abdulkadir Ibrahim,
G.C.L.C,KANO.