Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kunanan lafiya.
Bayan inason mika raayina akan irin gudunmawar da kasar Sin ke bawa kasashen AFIRKA , wannan magana tabbas ce idan aka kula da yadda tun daga fara aikin sabbin shugabannin kasar SIN sun kawo ziyara kasashe daban- daban na Afirka tare da basu taimako a fanni-fanni, Sannan akurkusa ziayarar shugabannin kasashen AFIRKA guda biyu wato na Nijireya da na kenya da suka kai kasar Sin da irin da alfanin da wannan ziyara ta kawo. Inafatan wannan alaka zata kara bunkasuwa ta yarda zaa kawar da kasashe yan babakere a Afirka.
Sannan a gaskiya naji dadin shirinku na jiya na inbaku wanda kuka tattauna da Hajiya inna Maryam Ciroma wato matar Malam Adamu Ciroma wacce ta karanta kimiyyar Siyasa tare da yin gwagwarmaya lallai wannan mata jarumace abin kwatance, na karu sosai cikin wannan hira musammam yadda kusa mun karanta abu daya a makaranta.
Nagode. Xie Xie.
ABDULKADIR IBRAHIM.
G.C.L.C.KANO.