in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2011-07-19 17:41:39 cri

Sanusi: To, jama'a masu sauraro, barka da dawowa a cikin shirinmu na Gani Ya Kore Ji. A cikin bayaninmu da ya gabata, mun bayyana muku yadda aka samar da matsuguni ga makiyaya a jihar Xinjiang. Yanzu ni da malam Ibrahim za mu ci gaba da tattaunawa kan yadda ake bunkasa sha'anin ba da ilmi a jihar Xinjiang.

Ibrahim: To, jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara wata wakar yara ce da ta samu karbuwa a kasar Sin. Yaran da suke wani gidan renon yara na garin Duoluo na gundumar Luopu ta jihar Xinjiang ne suka rera wannan waka. A cikin wannan gidan renon yara, ana koyar da ilmi da yaren wurin da harshen Han. Lokacin da wakilanmu suke neman labaru a jihar Xinjiang, sun gano cewa, al'ummomin kabilu dadan daban suna maraba da irin wannan kokari, wato yadda ake amfani da yaren kabilu daban daban na jihar Xinjiang, da kuma harshen Han wajen koyar da yara a makaranta.

"Sannu, malama."

Sanusi: Lokacin da wakilanmu suka shiga wani aji na gidan renon yara dake karkashin makarantar firamare ta garin Duoluo, kananan yaran da suke karatu sun gai da su nan da nan da harshen Han. Malama Nurbia Asan tana koyar musu harshen Han. Ta gaya wa wakilanmu cewa, dukkan yaran da suka fito daga kauyukan kabilar Uygur na wurin. Kafin su shiga gidan renon yara, ba su taba koyon harshen Han ba, sun iya yaren Uygur ne kawai. Malama Nurbia ta ce, "A da, yaran da suke zaune a kauyuka sun yi fatan koyon harshen Han ne bayan sun shiga aji uku na makarantar firamare. Kuma su kan koyi ilmin nahawun harshen Han, amma ba su iya magana da harshen Han ba. Amma yanzu, tun daga gidan renon yara sun soma koyon harshen Han. Suna da sha'awa, kuma suna kokarin koyon wannan harshe matuka."

Ibrahim: Na ji an ce, a da, sakamakon rashin isassun malamai wadanda suka kware a harshen Han da yarurukan kabilu daban daban na jihar, a cikin dogon lokacin da ya gabata, mutanen da suke zaune a kauyukan jihar Xinjiang ba su iya harshen Han ba. Sakamakon haka, ba su koyi ilmin kimiyya da fasaha ba, balle mallakar fasahohin zamani na bunkasa tattalin arziki da inganta zaman rayuwarsu.

Sanusi: E, haka ne. Yawan mutanen kabilar Uygur da suke zaune a garin Duoluo na gundumar Luopu ya kai kashi 96 cikin kashi dari bisa jimillar yawan mutanen garin. Shugaba Abdul Rayim na makarantar firamare ta Duoluo ya ce, idan yara sun iya magana da harshen Han, wannan zai iya taimaka musu wajen neman aikin yi da samun karin ilmi a nan gaba. Mr. Abdul Rayim ya ce, "Yanzu, zaman al'umma tana samun ci gaba cikin hanzari. Bayan da aka kyautata ingancin aikin ba da ilmi a gidajen renon yara, kuma wannan mataki zai taimaka wajen kyautata ingancin aikin ba da ilmi a makarantun firamare da sakandare da kuma jami'o'i."

Ibrahim: Jama'a masu sauraro, lokacin da wakilanmu suke neman labaru a jihar Xinjiang, sun samu labari cewa, ya zuwa shekarar 2012, za a koyar da harshen Han a gidajen renon yara da yawansu zai kai kashi 85 cikin kashi dari. Mun amince da cewa, bayan yaran wurin sun lakanci harsunansu da Han gaba daya, tabbas za su iya taka muhimmiyyar rawa wajen raya tattalin arziki da inganta zaman rayuwarsu gaba daya. (Sanusi, Ibrahim Yaya)


1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China