in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2011-07-19 17:41:39 cri

Sanusi: jama'a masu sauraro, filin ciyayi na Nalati na yankin Yili na Khazak dake yammacin jihar Xinjiang ta kasar Sin wurin yawon shakatawa ne da ya yi suna sosai. Kuma tun fil azal, shahararren filin ciyayi ne na kiwon dabbobi. Amma a ganin Cari Beard, wanda ya kai shekaru 16 da haihuwa, wato yaron makiyaya Beard Buick, zaman rayuwar makiyaya ba shi da dadi balle ya kasance abin nishadi da masu yawon shakatawa suke ji.

Ibrahim: Malam Sanusi, ka sani, tun fil azal makiyayan kabilar Khazak wadanda suke zaune a wurin su kan zauna a wurin dake da ciyayi, wato idan akwai ciyayi a wani wuri, sai su zauna a wannan wuri tare da shannu da tumaki da sauran dabbobinsu. A lokacin da ruwan sama na dusar kankara ya soma narkewa, makiyaya su kan tafi da dukkan iyalansu da dabbobinsu zuwa wani filin ciyayi, sannan a lokacin zafi, lokacin da dusar kankara dake kan dutse ya fara narkewa, sai su je filin ciyayin dake saman dutse. Amma a lokacin sanyi, su kan koma wani wurin don maganin sanyi tare da iyalansu da dabbobinsu. Ba ma kawai irin wannan zaman rayuwar makiyaya ba ta dacewa da zaman rayuwar zamani ba, har ma su kan sha wahala sosai. Lokacin da take tunawa da irin wannan zaman rayuwa, malama Hartung Bazkhuzi, mahaifiyar Cari Beard ba ta ji dadi ba, inda ta bayyana cikin harshen Khazak, cewar "Mu kan sha wahala sosai sabo da mu kan kaura a kullum. Yara su kan fuskanci matsala wajen shiga makaranta, sannan tsoffi ma su kan gamu da matsala wajen ganin likita. Dole ne mu yi amfani da doki inda muke shafe kimanin sa'o'i daya ko biyu domin kai su makaranta ko asibitin dake cikin gari. Idan mun je wani wurin dake nesa da garin, sai hankalinsu ya kwanta. Yanzu an tsugunar da mu a wannan wuri, ba za mu gamu da irin wadannan matsaloli ba. Haka kuma yanzu akwai ruwan sha da wutar lantarki a cikin gidajenmu. Muna farin ciki kwarai."

Sanusi: Tun karshen karnin da ya gabata, karamar hukumar Nalati ta soma sa kaimi ga makiyaya da su zauna a wuri daya, har ma ta taimake su wajen gina musu gidaje. Makiyaya da yawa sun amince da wannan shawara, kuma suna da wani gida a cikin gari. Mr. Li Gang, wanda ke kula da harkokin makiyaya da bunkasa tattalin arziki a karamar hukumar Nalati ya ce, "Tsarin zaman rayuwar makiyaya na gargajiya ya haifar da matsaloli da yawa. Da farko dai, ba a iya kula da koshin lafiyar iyalai, balle yara su samu ilmi. Sannan, makiyaya su kan zauna a cikin duwatsu, ba su iya samun wutar lantarki, balle zaman rayuwar zamani. Haka kuma, yawan kudin shiga da suke samu kalilan ne. A cikin shekaru 2 da suka gabata, mun sa kaimi ga makiyaya da su zauna a wani wuri, sannan sun sauya salon kiwon dabbobi na gargajiya. Bugu da kari, muna kokarin bunkasa sha'anin yawon bude ido a yankin Nalati domin kokarin tabbatar da ingancin filin ciyayi da kuma kara yawan kudin shiga na makiyaya."

Ibrahim: Beard Buick da iyalansa 7 sun zama daya daga cikin iyalai wadanda suka riga sauran makiyaya zauna a waje guda. Bayan sun koma matsuguninsu, sabo da gidansu yana kusa da garin Nalati, yanzu yara da tsoffinsu sun samu sauki sosai wajen shiga makaranta da zuwa asibiti. Bugu da kari, yanzu akwai ruwan sha da wutar lantarki a cikin gidansu, suna jin dadin zamansu. Haka kuma, yanzu yawan dabbobin da Beard Buick da iyalansu suke kiwo ya karu sabo da gwamnatin wurin ta taimaka musu da dabarun kiwon dabbobi na zamani. Beard Buick ya yi farin ciki ya gaya wa wakilanmu cikin harshen Khazak, cewar "Yanzu ina da tumaki fiye da dari 1, shannu 30 da doki 20. Zaman rayuwata ya ingantu kwarai."

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China