in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2011-07-19 17:41:39 cri

Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar Sin ta kuduri aniyar tallafawa jihar ta yadda tattalin arziki da zaman rayuwar jama'ar wurin za su bunkasa.

A karkashin wannan tsarin kasar Sin za ta kashe kudin Sin Yuan biliyan 120 zuwa 150 wajen gina hanyoyi a yammacin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa cikin shekaru biyar masu zuwa.

Sannan, gwamnatin yankin ta ce za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin hanyoyi da gyara tsoffin da ake da su don taimakawa ci gaban yankin kamar yadda gwamnatin tsakiya ta yi alkawari a bara.

A halin yanzu gwamnatin yankin Xinjiang ta bullo da sabbin hanyoyin kara samar da guraban aikin yi ga wadanda ba su da aikin yi a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa ta yadda za a samar wa mutane sabbin guraban aikin yi don su inganta rayuwarsu, kuma ana fatan wannan shirin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin.

A halin da ake ciki kuma malam Sanusi da sauran masu sauraronmu, gwamnatin kasar Sin ta gina rukunin gidaje sama da dubu 150 inda aka raba su kyauta ga wasu magidanta a garin Kashi baya ga kasuwar zamani da wurin Ibada da ofishin ba da hidima ga mazauna unguwar da aka gina.

Sanusi: To, malam Ibrahim, dazu ka ce, gwamnatin tsakiya da gwamnatin yankin suna kokarin gina gidaje sama da dubu 150 inda aka raba su kyauta ga wasu magidanta a garin Kashi. A kwanan baya, wasu wakilanmu na gidan rediyon CRI sun je jihar inda suka farauto mana labari cewa, ba ma kawai gwamnatin yankin na kokarin samar wa mazauna garin Kashi gidaje kyauta ba, har ma tana kokarin gina wa makiyaya gidaje a kokarin da take na tsugunar da su a waje guda

Ibrahim: Wannan wani babban albishir ne. Malam Sanusi, ko za ka iya bayyana wa masu sauraronmu wannan bayani filla filla.

Sanusi: ko shakka babu, zan bayyana wa masu sauraronmu wani bayanin da wakilanmu suka ruwaito mana kan yadda aka gina wa makiyaya na jihar Xinjiang gidaje domin warware matsalar muhalli da suke fuskanta a kullum

"A da, mu kan zauna a saman tudu ne. Sakamakon haka, na kan dauki dogon lokaci kafin na isa makaranta. A kowace rana, tun kafin gari ya waye ni da mahaifina mu kan hau doki daga gida zuwa makaranta, sannan ya kan zo ya dauke ni bayan an tashi daga makaranta a kowace rana. Sabo da haka, na kan shafe sa'o'in kimanin 3 a kan hanyar zuwa makaranta. Ka san cewa a kan yi ruwan sama na dusar kankara a lokacin sanyi. Wata rana, ba mu iya saukowa daga inda muke sakamakon dusar kankara mai tsanani. Sakamakon haka, ban je makaranta ba har na tsawon rabin wata."

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China