in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2011-07-19 17:41:39 cri

Sanusi: Malam Ibrahim, ka sani, ba kawai Beard Buick yana kiwon dabbobi ba yanzu, yana kuma yin wani aiki daban domin neman karin kudi.

Ibrahim: Shi makiyayi ne, ban da kiwon dabbobi, menene yake yi yanzu?

Sanusi: A shekarar bara, ya kashe kudin da ya samu a cikin 'yan shekarun nan, inda ya sayi wata motar daukar kaya. A yayin da yake sufurin ciyayi da dabbobinsa, yana kuma sufurin sauran kayayyaki. Sakamakon haka, yawan kudin da ya samu ya karu cikin hanzari, wato yanzu yawan kudin shiga da yake samu a kowace shekara ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu 50.

Ibrahim: Lallai, wannan makiyayi yana da dabarar hanyoyin samun kudi. Malam Sanusi, a cikin bayaninmu na baya, mun bayyana cewa, filin ciyayi na Nalati wuri ne na yawon shakatawa. Yaya ake bunkasa yawon shakatawa a wurin, kuma mene ne dangantakar dake tsakanin sha'anin yawon shakatawa da makiyaya?

Sanusi: Wannan tambaya ce mai kyau. Malam Ibrahim, gwamnatin wurin na kokari sosai wajen raya sha'anin yawon shakatawa a filin ciyayi na Nalati. Bisa kokarinsu, yanzu wannan wuri ya zama daya daga cikin wuraren yawon shakatawa mafi kyau a jihar Xinjiang, sakamakon haka, yawan masu bude ido da suke zuwa yawon shakatawa filin ciyayi na Nalati ya karu cikin hanzari. Kuma lokacin da take kokarin bunkasa sha'anin yawon bude ido a wurin, gwamnatin wurin ta sa kaimi ga makiyaya da su halarci ayyukan da suke da nasaba da sha'anin yawon shakatawa. Alal misali, yanzu yarinya Rena Beard, wato wata 'yar Beard Buick tana taka rawa a cikin kungiyar nune-nunen kide-kide da raye-raye ta Nalati, inda Rena Beard ta bayyana cikin harshen Khazak, cewar "Sunana Rena Beard. Na kai shekaru 19 da haihuwa. A da, ni makiyayiya ce, amma yanzu 'yar rawa ce. Na fi son wannan sana'a ta rawa. Yanzu albashina ya kan kai kudin Sin yuan dubu 2 a kowane wata."

Ibrahim: To, malam Sanusi, yanzu bari mu shakata kadan. Sannan a daga bisa za mu tattauna kan yadda ake bunkasa sha'anin ba da ilmi a jihar Xinjiang.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China