in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
2011-07-19 17:41:39 cri

Sanusi: A bara, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta shirya wani babban taro game da batun bunkasa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. To, yanzu a wane irin halin da al'ummomin jihar suke ciki? Kuma wane irin ci gaba aka samu a jihar a fannoni daban daban? Yau, na gayyaci abokin aikina malam Ibrahim Yaya wanda ya taba kai ziyara a jihar Xinjiang a bara don mu tattauna wadannan batutuwa, musamman batun yadda makiyaya na jihar suka samu wurin kwana, da batun bunkasa harkokin ba da ilmi a jihar. To, malam Ibrahin Yaya, da farko dai, ko za ka iya bayyana wa masu sauraronmu kadan daga cikin abubuwan dake da muhimmanci a jihar Xinjiang?

Ibrahim: To, malam Sanusi. Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin ne , kuma ta yi iyaka da kasashe takwas, ciki har da Rasha da Kazakhstan da Kyrghizstan da Tajikistan da Pakistan da Mangoliya da Indiya da kuma Afghanistan.

Haka kuma, Fadin jihar Xinjiang ya kai murabba'in kilomita miliyan 1 da dubu 660, wanda ya kai kashi daya daga cikin kashi shida na fadin kasar Sin baki daya, abin da ya sanya jihar a matsayin jiha mafi fadi a kasar Sin.

Sanusi: e, malam Ibrahim. Bugu da kari, Allah ya albarkaci jihar Xinjiang da albarkatun kasa kamar Tagulla da Dalma da Kwano da Kwal da Azurfa da Zinare da sauransu baya ga koramu da tabkuna da sauran halittu. Har ila yankin Xinjiang ya yi suna wajen samar da 'ya'yan itatuwa kamar Lemo da Inabi da Tufa baya ga Alkama da kuma Auduga da ake nomawa a yankin.

Ibrahim: Sannan, wani batu malam Sanusi shi ne, yawan mutanen dake jihar ya kai kimanin miliyan 20 da dubu 951, kuma daga cikinsu, kashi 60.7 cikin 100 sun kasance 'yan kananan kabilu ne. Tun zamanin da, Xinjiang wuri ne da kabilu da dama ke zaman cude-ni-in-cude-ka, kuma a halin yanzu Xinjiang tana da kabilun da yawansu ya kai 47, musamman ma kabilu 13 wadanda suka fara zama a jihar tun kaka da kakanni, ciki har da Uygur da Han da Kazak da Hui da Khalkhas da Mongoliya da Tajik da Xibe da Man da Uzbek da Rasha da kuma Tartar.

Sanusi:Malam Ibrahim, Na ji an ce, jihar Xinjiang jiha ce mai arzikin wuraren yawon shakatawa, ko za ka iya bayyana mana yaya ake raya harkokin yawon shakatawa a jihar?

Ibrahim: To, alkaluma sun nuna cewa, a farkon rabin shekarar 2010 yawan masu yawon shakatawa daga gida da ketare da suka ziyarci jihar ya kai miliyan 10, wannan ya karu da kashi 9 cikin 100 bisa na shekarar 2009, kuma yawan kudin da aka samu daga yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 10.2, wannan adadi ya karu da kashi 10 cikin 100 bisa na shekarar 2009. Wani muhimmin abu da ya kasance a jihar ta Xinjiang shi ne na tsauni mafi girma na biyu a duniya mai tsayin mita dubu 8 da 511 dake kudu da Xinjiang a iyaka da kasar Pakistan. Sannan akwai tsoffin wuraren tarihi da yawansu ya kai kimanin 236.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China