in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF za ta samar da guraben ilmi ga yara dubu 9 a birnin Benghazin kasar Libya
2019-05-16 10:01:35 cri
Asusun tallafawa ilmin kananan yara na MDD (UNICEF) ta sanar da cewa za ta samar da damammakin karatu ga kananan yara da matasa 9,000 a birnin Benghazi dake gabashin kasar Libya.

Hukumar ta UNICEF ta bayyana cewa, "Tare da hadin gwiwar kungiyar Ekraa, yara da matasa 9,000 a birnin Benghazi ne za su samu damammakin guraben karatu domin kyautata makomar rayuwarsu."

A cikin wannan sanarwa, an kuma nuna cewa, "Yarjejeniyar ta shekara guda za ta samar da damar karatu ga yara mata da maza ba tare da yankewa ba wadanda riciki ya shafa, haka zalika, shirin zai taimakawa yaran da ba su samu damar halartar darrusan share fagen shiga jami'a ba inda za su samu damar koya don kamo takwarorinsu."

Benghazi, shi ne birni na biyu mafi girma a kasar Libya, kuma a can ne aka kafa tushen zanga zangar 2011 wacce ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, ana ci gaba da fuskantar tashin hankali tsakanin bangaren dakarun sojojin dake da sansani a gabashin kasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini.

A watan Yunin shekarar 2017, Haftar ya sanar da kwace ikon Benghazi tare da yin galaba kan kungiyoyin abokan gaba a birnin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China