in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da mummunan harin da kungiyar IS ta kai kudancin Libya
2019-05-05 16:02:59 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya (UNSMIL) ya yi tir da mummunan harin da mayakan IS suka kai kan cibiyar horar da sojoji a birnin Sabha na kudancin Libya.

Shirin ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da IS ta dauki alhakin kai wa, wanda ya rutsa da mutane da dama.

Sanarwar da shirin ya fitar, ta ce ya zama wajibi a hukunta maharan da masu kitsa hare haren da masu samar musu da kudi da kuma masu daukar nauyinsu.

Ta ce wannan harin na tunatar da al'ummar Libya da ma na duniya baki daya cewa, kungiyoyin ta'adda za su yi amfani da duk wata dama da suka samu, ciki har da rikicin Tripoli, wajen fadada kasancewarsu a kasar.

Shirin ya yi kira ga bangarorin Libya, su kauracewa kara ta'azzarar matakan soji tare da mayar da hankali kan kokarin yaki da kungiyar ta'adda dake zaman makiyarsu baki daya.

Kungiyar IS ta dauki nauyin kai hari kan cibiyar horar da soji a birnin Sabha, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 9. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China