Hukumar kwastam mai buga haraji karkashin majalissar zartaswar kasar ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, wadanda suka gabatar da bukatar dage musu karin harajin, za su iya cimma nasarar samun hakan ne kawai, idan sun gabatar da gamsassun dalilai, na ko dai rashin madadin irin wadannan hajoji, ko matsanancin yanayi na tattalin arziki da za su iya fuskanta, ko mummunan tasiri da sashen masana'antun su zai fuskanta, ko tasiri maras kyau ga zamantakewar al'umma.
Bisa aniyar Amurka ta karawa hajojin Sin da darajar su ta kai dala biliyan 200 harajin kaso 25 bisa dari daga kaso 10 bisa dari, tun daga ranar 10 ga watan Mayun bana, a jiya Litinin ita ma Sin ta sanar da aniyar kara harajin ta ga hajojin Amurkar da ake shigarwa Sin, tun daga ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa.
Gabanin hakan Sin ta kara haraji kan wasu hajojin Amurka da darajar su ta kai dala biliyan 60, kana za ta sake kara wa irin wadannan hajoji harajin kaso 25 da kaso 20 da kuma kaso 10 bisa dari. (Saminu Alhassan)