in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan aiwatar da tsarin tantance matafiya kai tsaye ta na'ura a manyan filayen jiragen sama
2019-05-13 10:14:42 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar Sin, ta ce kasar ta daura damarar inganta tsarin tantance matafiya da kayansu kai tsaye ta hanyar amfani da na'ura a manyan filayen jiragen sama, da nufin inganta ayyuka a filayen jiragen, saboda karuwar matafiya.

A cewar hukumar, a shekarar 2019, ya kamata dukkan filayen jiragen sama dake samun fasinjoji miliyan 10 a shekara, su yi kokarin fadada hidimar tantance matafiya da kayansu ta nau'ra ga fasinjoji sama da kaso 70 cikin dari.

Hukumar ta ce tantance matafiya da kayansu ta na'ura, babban yunkuri ne dake da nufin tabbatar da aminci da ingancin ayyuka a manyan filayen jiragen sama, yayin da ake tsaka da fuskantar karuwar matafiya.

A bara, jimilar tafiye-tafiyen miliyan 225 aka yi ta hanyar amfani da na'ura wajen tantance bayanan matafiya, wanda ya rage sa'o'i miliyan 18.75 na jira.

Ya zuwa karshen 2018, kasar Sin na da jimilar filayen jiragen sama masu lasisi 235, daga cikinsu kuma 37 na samu fasinjojin da yawansu ya kai miliyan 10 a shekara.

Yanzu kasar Sin ce kasa ta biyu mafi girman kasuwar sufurin jiragen sama. A bara, an gudanar da tafiye-tafiye miliyan 610 ta jiragen sama a kasar, adadin da ake sa ran zai karu zuwa miliyan 680 a bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China