in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu He: hadin gwiwa ya fi dacewa, amma Sin ba za ta amince da manyan batutuwan dake kawo barazana gare ta ba
2019-05-12 17:07:13 cri
An gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka zagaye na 11 a birnin Washington na kasar Amurka tun daga ranar 9 zuwa 10 ga wannan wata. Bayan shawarwarin, manban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma mataimakin firaministan kasar Sin kana jagoran tawagar Sin a shawarwarin Liu He ya bayyanawa 'yan jarida cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana da muhimmanci sosai, dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu tushe ne na raya dangantakar dake tsakaninsu, wadda ita ma ta shafi kiyaye zaman lafiya da samun wadata a duniya. Hadin gwiwa hanya daya kawai mafi dacewa ce, an yi hadin gwiwa bisa ka'idoji, kana Sin ba za ta amince da manyan batutuwan dake kawo barazana gare ta ba.

Liu He ya bayyana cewa, Sin tana da sahihanci da yin shawarwari da kasar Amurka a birnin Washington, kana bangarorin biyu sun amince da ci gaba da yin shawarwarin. Sin ta ki amincewa da kara buga harajin kwastam da Amurka ta yi, wanda zai kawo illa ga moriyar kasar Sin da kuma ita kanta Amurkar, har ma da duniya baki daya, don haka Sin za ta dauki matakan mayar da martani.

Liu He ya jaddada cewa, tilas ne bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya cikin adalci da samun moriyar juna, kana Sin ba za ta amince da manyan batutuwan dake kawo barazana gare ta ba. A halin yanzu, bangarorin biyu sun cimma daidaito kan fannoni da dama, amma tilas ne a daidaita batutuwa uku da Sin ta fi sa lura kansu. Na farko, soke dukkan karin harajin kwastam da aka buga. Na biyu, yawan kudin da aka kashe a ciniki ya yi daidai, bangarorin biyu sun riga sun cimma daidaito kan yawan kudin da aka kashe kan cinikinsu a kasar Argentina, bai kamata a canja shi ba. Na uku, kyautata yarjejeniyar cikin daidaici. Ya kamata a girmama dukkan kasashe, tilas ne a cimma yarjejeniya cikin daidaito, yanzu ana bukatar tattaunawa kan wasu batutuwan dake cikin yarjejeniyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China