in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasa Sinawa na da kwarin gwiwar cimma nasarar gina kasarsu a cewar wani bincike
2019-05-13 12:38:57 cri

Sakamakon wani binciken baya bayan nan da wata kungiya ta gabatar ya nuna cewa, da yawa daga matasa Sinawa, na da karfin gwiwar cimma nasarar gina babbar kasar Sin mai bin salon mulkin gurguzu, wadda za ta kasance mai wadata da biyayya ga dimokuradiyya, da kyawawan al'adu, da zaman lumana, da kayatarwa nan da tsakiyar wannan karni.

Masu binciken sun tuntubi mutane da yawansu ya kai 10,393 daga larduna 31 na kasar, wadanda kaso 67.4 bisa darinsu aka haifa a ciki, ko bayan shekarar 1990.

Sakamakon wani binciken da aka gabatar yayin taro na 19 na majalissar wakilan JKS cikin watan Oktoban 2017 ya nuna cewa, akwai bukatar aiwatar da manyan matakai biyu, domin daga matsayin kasar Sin zuwa kasa mai bin salon mulkin gurguzu, wadda za ta kasance mai wadata, da biyayya ga dimokuradiyya, da kyawawan al'adu, da zaman lumana, da kayatarwa nan da tsakiyar wannan karni.

Sakamakon jin ra'ayin ya nuna cewa, wadanda aka zanta da su sun bayyana maki 8.92 cikin 10 na karfin gwiwar cimma wannan buri, inda kaso 50.8 bisa dari na matasan suka baiwa manufar maki 10 baki daya.

Har ila yau, sakamakon ya nuna cewa, wasu matasan da aka haifa a ciki, ko bayan shekarar 2000 sun ba da maki 9.16 bisa 10 na karfin gwiwar da suke da shi, wanda shi ne kaso mafi yawa da aka samu tsakanin matasan. Kaza lika matasan dake zaune a yankunan karkara sun ba da makin da ya kai kaso 9.04 bisa 10, wanda hakan ya dara na mazauna yankunan birane.

Da yake tsokaci game da hakan, masani a fannin kimiyyar zamantakewar al'umma a kwalejin kimiyyar kasar Sin Gong Yun, ya ce al'ummar Sinawa na da yakinin cewa, ci gaban kasarsu zai samu ne ta hanyar cimma manufofin da gwamnati ke aiwatarwa, da jagoranci daga akidun Markisanci, da kasancewar al'ummar kasar masu jajircewa wajen ginin kasa da al'ummarta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China