in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da sanarwar kara harajin kwastam ga wasu kayayyakin da Amurka da ke shiga kasar Sin
2019-05-13 21:46:58 cri

A ranar 9 ga wannan wata, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, tun daga ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2019, za ta kara harajin da take karba kan kayayyakin Sin da ke cikin jerin kayayyakin da Amurka ta gabatar da darajarsu ta kai dala biliyan 200 daga kashi 10 cikin dari zuwa 25 cikin dari. Matakin na Amurka ya tsananta matsalar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, wanda ya saba matakan da Sin da Amurka suka cimma ta hanyar yin shawarwari, da kawo illa ga muradunsu da kuma sabawa begen kasa da kasa a wannan fanni. Don tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da moriyar juna, Sin ta tsaida kudurin kara sanya harajin kwastam kan wasu kayayyakin Amurka.

Bisa abubuwan da aka tanada cikin Dokar cinikayyar waje ta kasar Sin da Ka'idojin harajin kwastam na kayayyakin shigi da fici na kasar, bayan da ya samu amincewa daga kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar, kwamitin kula da ka'idojin harajin kwastam na majalisar ya tsai da kudurin cewa, tun daga ranar 1 ga watan Yuni, kasar Sin za ta kara yawan harajin da ta saba karba kan wasu kayayyakin Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 60 wadanda kasar Sin ta riga ta kara musu harajin a baya, wato za a karawa kayayyakin harajin da ya kai kaso 25, kaso 20 ko kuma kaso 10. Game da kayayyakin Amurka da Sin ta riga ta kara musu harajin da kaso 5, za a ci gaba da karbar harajin.(Zainab, Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China